Yadda dakarun Nijeriya suka kama wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargi da ta’addanci a arewa maso gabas

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Dakarun Operation HADIN KAI sun kama wani ɗan ƙasar Sudan da ake zargin yana da alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci, tare da cafke wasu mutum uku da ake zargi masu haɗa kai da ƙungiyar ISWAP da kuma samar mata da kayan aiki a hare-haren da suka gudanar a jihohin Borno da Yobe.

Rahotannin ayyukan soji da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya samu a ranar Litinin sun bayyana cewa kamen ya biyo bayan bayanan sirri da dakarun suka samu, wanda ya kai ga gudanar da farmaki a wurare daban-daban na yankin Arewa maso Gabas.

Rahoton ya ce dakarun Bataliya ta 115 sun kama wani ɗan Sudan mai suna Musa Fashir, mai shekara 32, a yankin Lassa-Dille da ke ƙaramar hukumar Askira/Uba ta jihar Borno.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin Fashir na da alaƙa da wasu ‘yan ta’adda, lamarin da ya ƙara nuna yiwuwar shigowar mayaƙan ƙasashen waje domin taimaka wa ayyukan ta’addanci a yankin.

Haka kuma, dakarun sun kama wata mata mai suna Mary Florence, mai shekara 36, wadda ta ce ita baƙuwa ce daga ƙasar Ghana ba tare da takardun izini ba. Jami’an tsaro na ci gaba da bincike domin tabbatar da asalinta da kuma ko tana da wata alaƙa da ayyukan ta’addanci ko wasu laifuka.

A wani samame daban, dakarun Brigade ta 27 tare da haɗin gwiwar Civilian Joint Task Force (CJTF) sun kama wani da ake zargin mai haɗa kai ne da ISWAP a yankin Shishiwaji da ke ƙaramar Hukumar Gulani ta jihar Yobe.

Rahoton ya ce ana zargin mutumin mai haƙar ma’adinai ne ba bisa ƙa’ida ba, kuma yana da alaƙa da ISWAP. An kama shi da wayoyin hannu guda uku.

Har ila yau, yayin sintirin kare manoma a yankin Kasabalari da ke ƙaramar hukumar Damboa ta jihar Borno, dakaru sun kama wasu mutum biyu da ake zargin suna samar wa ISWAP kayan aiki.

Kayan da aka ƙwato daga hannunsu sun haɗa da kekuna biyu, wayar hannu guda ɗaya, katin shaida, magungunan kashe kwari, magunguna, kayan gyaran keke, na’urar hasken rana (solar panel), fitilar hannu da kuma wuƙaƙe.

Jami’an sojin sun bayyana cewa waɗannan nasarori sun nuna yadda amfani da bayanan sirri ke taimakawa wajen dakile shigowar mayaƙan ƙasashen waje, rushe hanyoyin samar da kayan aiki ga ‘yan ta’adda da kuma karya cibiyoyin masu mara musu baya a yankin Arewa maso Gabas.

By ukarofi

Leave a Reply