An buƙaci iyayen yara Musulmi a Legas su ƙara ba ilimin addini da na zamani muhimmanci

Spread the love

Daga DAUDA USMAN a Legas

An shawarci iyayen yara Musulmi a Jihar Legas da ma Nijeriya baki ɗaya da su ƙara ƙaimi wajen sanya ‘ya’yansu a makarantun koyar da Alƙur’ani Mai Tsarki da sauran ilimin zamani, domin su samu tarbiyya ta gari da ilimi mai amfani.

Wannan kira ya fito ne daga shugaban kula da ci gaban ɓangaren kasuwancin kayan ƙamshin Yarabawa a Kasuwar Mile 12 da ke Legas, Alhaji Abdulmummuni Cikada, ɗan asalin ƙaramar Hukumar Kiru ta Jihar Kano.

Ya yi wannan kira ne yayin da yake jawabi a taron bikin walimar yaye ɗalibai karo na biyar na Makarantar Tazakiya Islamiyya, wanda aka gudanar a harabar makarantar firamare da ke unguwar Mile 12 a ranar Lahadin da ta gabata.

Daga cikin ɗaliban da aka yaye akwai ‘ya’yansa biyu, Sumaiya Abdulmummuni Cikada da Ramlatu Abdulmummuni Cikada, waɗanda suka kasance cikin fitattun ɗaliban da suka yi fice a jarrabawar tantancewa tare da sauran abokan karatunsu.

Alhaji Abdulmummuni ya bayyana farin cikinsa bisa nasarar da ‘ya’yansa da sauran ɗaliban makarantar suka samu, inda ya ce yana godiya ga Allah Maɗaukakin Sarki da Ya ba shi ikon ba ‘ya’yansa ilimin addini tun daga farkon karatunsu har suka kammala wannan mataki cikin nasara.

Ya kuma taya shugabannin makarantar, malamai da iyayen ɗaliban murnar gudanar da wannan walima, tare da ƙarfafa wa ɗaliban gwiwa da su ci gaba da neman ilimi a manyan makarantu domin su zama abin alfahari ga iyayensu da al’ummarsu.

Shi ma Alhaji Abubakar Garba, wanda shi ne Sakataren ɓangaren Kasuwancin Kayan ƙamshin Yarabawa a Kasuwar Mile 12, ya bayyana farin cikinsa da gudanar da bikin.

Ya taya Alhaji Abdulmummuni Cikada, iyayen ɗaliban da aka yaye da kuma shugabannin makarantar murnar wannan nasara, yana mai fatan Allah Ya sanya ilimin da ɗaliban suka samu ya amfane su a rayuwarsu.

Haka kuma, ya yaba da irin jagorancin Babban Shugaban Kasuwar Mile 12 International Market, Alhaji Shehu Usman Jibrin Samfam, bisa ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da bunƙasa harkokin kasuwanci a kasuwar.

Ya kuma jinjinawa shugaban ɓangaren kayan ƙamshin Yarabawa, Alhaji Abdulmummuni Cikada, bisa yadda yake haɗa kan Hausawa da sauran ƙabilun da ke gudanar da kasuwanci a Mile 12, domin ƙarfafa zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban kasuwar baki ɗaya.

By ukarofi