Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Duk da ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Nijeriya, ciki har da hare-haren sama kan sansanonin ‘yan ta’adda da faɗaɗa musayar bayanan sirri, al’amuran tsaro a ƙasar na ci gaba da taɓarɓarewa, inda sabbin alƙaluma suka nuna cewa hare-haren ta’addanci da sauran nau’o’in tashin hankali sun ƙaru fiye da yadda aka zata.
A ranar Kirsimeti ta shekarar 2025 ne jiragen yaƙin Amurka suka kai hare-hare kan sansanonin mayaƙan ƙungiyar ISIS da ke Jihar Sakkwato, lamarin da ya nuna sabon mataki a yaƙin da Nijeriya ke yi da ta’addanci. Ko da yake Amurka ta daɗe tana tallafa wa Nijeriya a wannan fanni, hare-haren sun zama na farko cikin jerin farmakin da gwamnatin Washington ta ce ta ƙaddamar domin mayar da martani kan abin da ‘yan majalisar dokokin ƙasar suka bayyana a matsayin “kisan kiyashin Kiristoci” da ƙungiyoyin masu tsattsauran ra’ayi suka yi a Nijeriya.
Sai dai, watanni bayan wannan ƙawance ya ƙara ƙarfi, har yanzu tsaro bai inganta yadda ake fata ba.
Alƙaluman Armed Conflict Location & Eɓent Data Project (ACLED), wata cibiyar Amurka mai sa ido kan rikice-rikice a duniya, sun nuna cewa daga watan Janairu zuwa Yulin 2026, an samu hare-hare da rikice-rikice 5,918 a Nijeriya, adadin da ya kai kusan kashi 80 cikin 100 na duk hare-hare 7,539 da aka samu a shekarar 2025 baki ɗaya.
Rahoton ya kuma nuna cewa waɗannan hare-haren sun yi sanadin mutuwar mutane 10,904, adadin da ya kai kashi 73.2 cikin 100 na jimillar waɗanda suka mutu a duk shekarar 2025.
Masana sun yi gargaɗin cewa idan aka ci gaba da wannan yanayi, shekarar 2026 za ta iya zama mafi muni ta fuskar matsalar tsaro.
A cewar masu nazari, wannan ya haifar da wani babban tambaya: me ya sa matsalar tsaro ke ƙara tsananta duk da ƙarin tallafin soja daga ƙasar da ake kallon ita ce mafi ƙarfin soji a duniya?
Nijeriya dai ta sha bayyana cewa matsalolin tsaronta sun fi abin da ake danganta su da rikicin addini kaɗai. A cewarta, ƙasar na fama da matsaloli daban-daban da suka haɗa da ta’addancin da ke shigowa daga ƙasashen Sahel, ayyukan ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, ƙungiyoyin Boko Haram, ISWAP da ISIS, rikicin manoma da makiyaya, ƙungiyoyin asiri da sauran su.
Wani babban jami’in soja ya bayyana wa jaridar cewa matsalar tsaron Nijeriya tana da sarkakiya matuƙa.
Ya ce duk da cewa Amurka ta ƙara matsa lamba da taimakon soja, yawancin ƙoƙarinta ya fi karkata ne wajen yaƙi da Boko Haram da ISWAP, ba wai sauran matsalolin tsaro da suka addabi ƙasar ba.
A cewarsa, hare-haren sama kaɗai ba za su iya kawo ƙarshen matsalar ‘yan bindiga ba.
Ya bayyana cewa kashe wasu fitattun shugabannin ‘yan bindiga ta hanyar hare-haren sama ya sa ƙungiyoyinsu suka rarrabu zuwa ƙananan ƙungiyoyi masu zaman kansu, waɗanda yanzu ke fafatawa da juna tare da ƙara kai munanan hare-hare kan fararen hula.
Ya ce, “Idan aka kashe wani shugaban ‘yan bindiga, sai wasu sababbin shugabanni su fito su kafa sababbin ƙungiyoyi. Wannan ya sa rikicin ya ƙara rikicewa maimakon ya lafa.”
Duk da haka, jami’in ya amince cewa haɗin gwiwar Nijeriya da Amurka ya samar da wasu nasarori.
A watan Mayu, shugabannin ƙasashen biyu sun sanar da kashe Abu Bilal al-Minuki, wanda aka bayyana a matsayin mataimakin shugaban ISIS na biyu a duniya, yayin wani samamen haɗin gwiwa.
Har ila yau, jami’an Amurka sun ce kayan bayanan sirri da aka ƙwato daga wannan samame su ne mafi girma tun bayan harin 11 ga Satumba na shekarar 2001.
Tun daga wannan lokaci, ƙasashen biyu sun ci gaba da gudanar da wasu hare-hare da suka yi sanadin kashe mayaƙan ISWAP da dama.
Sai dai jami’in ya jaddada cewa mayaƙan ƙungiyoyin ta’addanci suna da ƙaramin kaso idan aka kwatanta da sauran matsalolin tsaron Nijeriya.
A cewarsa, idan har ana son kawo ƙarshen matsalar, dole gwamnati ta ɗauki wasu hanyoyi da suka wuce amfani da jiragen yaƙi.
Masana sun ce ‘yan bindiga sun zama babbar barazana ga tsaron ƙasar.
Hukumar Tarayyar Turai mai kula da harkokin mafaka (EUAA) ta bayyana cewa ayyukan ‘yan bindiga ba satar shanu kaɗai ba ne, sun haɗa da kisa, fyaɗe, garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa, fashi da makami da kai hare-hare kan al’ummomi.
Rahotanni sun nuna akwai fiye da ƙungiyoyin ‘yan bindiga 100 da ke aiki a yankin Arewa maso Yamma, tare da mayaƙa sama da 30,000.
Rahoton SBM Intelligence ya nuna cewa tsakanin Yulin 2024 zuwa Yunin 2025, an yi garkuwa da mutane 2,938 a Arewa maso Yamma, adadin da ya zarce kashi 60 cikin 100 na duk masu garkuwa da aka yi a faɗin Nijeriya.
Masu garkuwar sun nemi kuɗin fansa har Naira biliyan 48, kuma sun karɓi kusan Naira biliyan 2.57.
Masanin harkokin tsaro, Malik Samuel, ya ce sabanin ƙungiyoyin ta’addanci masu tsari, ‘yan bindiga ba su da shugabanci guda ɗaya, abin da ke sa ya zama da wuya a murƙushe su.
Ya kuma ce manyan dazuzzukan Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya sun zama mafakar ‘yan bindiga, inda suke komawa bayan kai hare-hare.
Baya ga haka, ya ce rashin isassun jami’an tsaro da kuma gazawar gwamnati wajen samar da muhimman ayyukan raya ƙasa na daga cikin manyan dalilan da ke ƙara tsananta matsalar.
A cewarsa, yankunan da ake fama da hare-hare su ne mafi ƙarancin samun ruwa, wutar lantarki, makarantu da cibiyoyin lafiya.
Ya ce hakan na bai wa ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai damar jawo hankalin wasu al’ummomi ta hanyar samar musu da wasu ayyukan da ya kamata gwamnati ce ke yi.
Masanan sun kuma soki yadda aka mayar da aikin tabbatar da tsaron cikin gida hannun sojoji, maimakon Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin farar hula.
Hakan ya ƙara ƙarfafa kiraye-kirayen kafa ‘yan sandan jihohi, bayan Majalisar Wakilai ta amince da ƙudirin gyaran kundin tsarin mulki domin kafa tsarin.
Wasu na ganin hakan zai taimaka wajen inganta tsaro saboda gwamnoni za su riƙa ɗaukar alhakin kare jihohinsu, yayin da jami’an tsaro za su fi sanin yankunan da suke aiki.
Sai dai wasu na fargabar cewa gwamnoni za su iya amfani da rundunar wajen cimma manufofin siyasa.
Masana sun yi ittifakin cewa ƙarfin soja da tallafin ƙasashen waje kaɗai ba za su wadatar ba wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro.
Sun ce sai an haɗa da ingantaccen shugabanci, adalci, bunaasa tattalin arziki, samar da ayyukan raya ƙasa da kuma ƙarfafa hukumomin tsaro kafin a samu dawwamammen zaman lafiya.
