Daga RABIU SANUSI a Kano
Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Hon. Hamza Sule Mai Fata, ya miƙa takardun naɗin aiki ga sabbin malamai 137 da aka ɗauka aiki a ƙarƙashin shirin SUBEB na dindindin mai fansho da kuma shirin Abba Gida Gida BESDA Cohort ɓ, inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin ƙaramar Hukumar na bunƙasa ilimi da ƙarfafa aikin koyarwa a faɗin yankin.
An gudanar da bikin ne a harabar Sakatariyar ƙaramar Hukumar Bichi, tare da halartar manyan jami’an gwamnati, shugabannin cibiyoyin ilimi, sarakunan gargajiya, jagororin siyasa, iyaye da sauran masu ruwa da tsaki, waɗanda suka bayyana shirin a matsayin wani muhimmin mataki na ƙara inganta ilimi da samar da ƙwararrun malamai.
Da yake jawabi yayin bikin, Hon. Hamza Sule Mai Fata ya taya sabbin malaman murnar samun aikin, yana mai bayyana cewa naɗin nasu ba kawai wata dama ta samun aikin yi ba ce, illa babbar amana ce ta gina makomar al’umma ta hanyar ilimi.
Ya ce gwamnati ta ɗora musu nauyin tarbiyya da ilimantar da yaran da za su zama shugabannin gobe, saboda haka ya buƙace su da su gudanar da aikinsu cikin gaskiya, riƙon amana, ƙwazo, ladabi da kishin aikin koyarwa.
Shugaban ƙaramar Hukumar ya kuma jaddada cewa halaye da ɗabi’un malamai na taka muhimmiyar rawa wajen gina ɗalibai nagari, yana mai cewa ya kamata su kasance abin koyi ga ɗalibai da al’umma baki ɗaya.
A nasa jawabin, Mataimakin Proɓost na Federal College of Education (FCE), Bichi, Dr. Kabiru Musa, wanda ya wakilci Proɓost ɗin jami’ar, ya tabbatar wa sabbin malaman cewa cibiyar za ta ci gaba da ba su cikakken goyon baya domin su samu nasara a aikinsu.
Ya bayyana cewa duk lokacin da buƙata ta taso, jami’ar za ta shirya musu shirin horaswa (Induction Programme) kyauta domin yara musu ƙwarewa da sabbin dabarun koyarwa da suka dace da tsarin ilimin zamani.
Dr. Kabiru Musa ya kuma yaba wa Gwamnatin Jihar Kano da yaramar Hukumar Bichi bisa ƙoƙarinsu na faɗaɗa damar samun ingantaccen ilimi da kuma samar da ayyukan yi ga ƙwararrun malamai.
Shi ma tsohon Mataimakin Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, Farfesa Armaya’u Hamisu, ya ce fifikon da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bai wa ilimi ya nuna aniyarsa ta gina ingantaccen tsarin ilimi a jihar.
Ya yaba wa Hon. Hamza Sule Mai Fata bisa shugabanci nagari, riƙon amana da aiwatar da shirye-shiryen ci gaba da suka amfani al’ummar Bichi kai tsaye.
A matsayin gudummawarsa ga sabbin malaman, Farfesa Armaya’u Hamisu ya ba da tallafin N200,000 domin yarfafa musu gwiwa yayin fara aikin gwamnati, tare da ƙarfafa musu guiwar su kasance jakadun nagarta, ƙwarewa da biyayya ga ƙa’idojin aikin koyarwa.
A nasa jawabin, Galadiman Kano, ta bakin wakilinsa Alhaji Abbas Bayero, ya yi kira ga sabbin malaman da iyayensu da su nuna godiya ga gwamnatin da ta ba su wannan dama, yana mai tunatar da su cewa dubban masu neman aiki sun yi burin samun irin wannan gurbi amma ba su yi nasara ba.
Ya jaddada cewa makomar al’umma tana hannun malamai, domin su ne ke da alhakin gina tunani, tarbiyya da ilimin matasa, waɗanda za su zama jagororin ƙasa a nan gaba.
An kammala bikin cikin farin ciki da addu’o’in fatan alheri ga Gwamna Abba Kabir Yusuf da Shugaban ƙaramar Hukumar Bichi, Hon. Hamza Sule Mai Fata, bisa ƙoƙarinsu na bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi da kuma inganta rayuwar al’ummar Bichi da Jihar Kano baki ɗaya.
