
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya amince da bayar da filaye ga masu taimaka masa, inda ya ce ya yi hakan ne da nufin rage matsalolin rashin gida, samar da wadata ga iyalai da kuma gina tubali mai kyau don gobe.
Waɗanda suka amfana da tagomashin sun haɗa da manyan masu taimakawa na musamman (SSAs), manyan maruwaita na musamman (SSRs), masu taimakawa na musamman (SAs), maruwaita na musamman (SRs) da masu taimakawa na kai-tsaye (PAs), kamar yadda Sakataren yaɗa labaran gwamnan, Mustapha Muhammad ya bayyana a wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.
Da yake jawabi yayin ƙaddamar da kyaututtukan a Babban Ɗakin Naɗi na Gidan Gwamnatin jihar (Coronation Hall) ƙarƙashin sanya idon Ma’aikatar Filaye da Tsare-tsare na Zahiri, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana bayar da filayen daga taswirar gwamnatin a matsayin gagarumar nasara ga waɗanda suka amfana.
Gwamnan, wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatinsa, Umar Ibrahim, ya ce an aiwatar da shirin ne da nufin inganta mallakar gida da bunƙasa tattalin arziƙi acikin ma’aikatan domin samun gobe mai kyau.
Ya ƙara da cewa, gwamnatinsa ta gamsu da cewa jagoranci na gari na tabbata ne a lokacin da aka cika alƙawuran da aka ɗauka, yana mai cewa hakan wani ɓangare ne na cika alƙawarin da suka yi wa makusantan nasa.
Ya kuma yaba musu bisa ƙoƙarinsu na tallafa wa gwamnatin nasa tun daga yaƙin naman zaɓe har zuwa yanzu, yayin da ta samu nasarori da dama.
Kazalika, ya yi kira a gare su da su riƙa ɗaukar kansu a matsayin jakadun gwamnatin ta hanyar wayar da kan al’umma kan tsare-tsaren da shirye-shirye da ayyukan da ake yi a ƙarƙashin gwamnatin Abba Gida-Gida.
