Yanzu-yanzu: Tinubu ya umarci EFCC ta buɗe asusun bankin gwamnatin Osun

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya umarci Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) ta gaggauta neman kotu ta soke umarnin rufe asusun gwamnatin Jihar Osun da kuma daina ɗaukar dukkan wani mataki akan jihar game da al’amarin.

Tinubu ya bayar da wannan umarni ne a wata takarda da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, 6 ga Agusta, 2026, inda ya ce ya ji takaici akan lokacin da hukumar ta ɗauki matakin, yana mai cewa ba ya inkarin ikon da dokar ƙasa ta ba EFCC na aiwatar da hukuncin saidai bai dace a yi hakan ba a irin wannan lokaci.

Shugaban ya bayyana haka ne ganin yadda ake ƙasa da kwanaki 10 na al’umma su kaɗa ƙuri’a a zaɓen gwamnan jihar.

Ya bayyana cewa, dukkan wani mataki da cibiyar gwamnatin tarayya za ta ɗauka, ana jingina masa ne kai-tsaye a matsayinsa na shugaba ko da kuwa bai da masaniya kan hakan.

Shugaba Tinubu ya jaddada cewa, tun lokacin da ya hau kan karagar mulki, yake bai wa hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa ikon gudanar da ayyukansu bisa yadda dokar ƙasa ta bayar da dama ba tare da tsoma baki ko sanya musu ido ba ko kuma ƙoƙarin siyasantar da lamuran nasu ba.

A cewarsa, hakan shi ne zai nuna cewa ƙasar na tafiya bisa jagorancin na gari da ciyar da harkokin dimukraɗiyya gaba wajen biyayya ga tsarin mulki.

By Babaji