
Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Bichi daga Jihar Kano, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar, ya ƙaddamar da buɗe tashar wutar lantarki da ake kira Farno-farno a ƙaramar hukumar.
A sanarwar da Jami’ar Yaɗa Labarai ta yankin, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta fitar, ta ce ya bayyana shekaru huɗu da suka wuce suke ta fafutukar yadda za a samar da tsayayyiyar wutarlantarkin a garuruwan mazaɓun yamma a garin Bichin, duba da ƙaruwar yawan jama’ar mazaɓun a halin yanzu, da hakan ya janyo matsalar rashin samun wuta yadda yakamata a yankunan.
Mazaɓun da suka haɗa da; Ɗanzabuwa, Ƙyalli, Ƙauƙau da kuma waire, Abban Bichi, ya taya su murna da kuma jan hankalinsu wajen mai da hankali ga bunƙasa sana’o’insu. Kazalika samar da wutar lantarkin ya haɗa da ƙananan hukumomin Tsanyawa da Ghari da ma Kasuwar Dawanau dake jihar Kano baki ɗaya.
“Wannan samar da wutar lantarkin zai ɗaga darajar waɗannan mazaɓu namu masu albarka, idan aka yi la’akari da sana’o’i da ake yi na yau da kullum tare da kuma sauran abubuwa na more rayuwa, kamar yadda mai gari ya faɗa ana kashe kuɗi masu yawa wajen zuba man fetur a ganareto da kuma ɓangaren masu haɗa sola, wasu ma da yawa ba su da halin da za su iya haɗa solar ko kuma kunna injin ganareton, amma cikin yardar Allah yau wuta za ta je gidan kowa, al’umma za su ji daɗin samun wannan wuta.” Ɗanmajalisa Abba Bichi.
Da yake jawabi Shugaban Kasuwar Zamani ta Bichi, Alhaji Garba Tukur, ya gode wa Allah bisa ni’imar da ya yi musu ta samun Ɗanmajalisar Tarayya Abba Bichi, inda a ƙarshe ya ƙarfafa gwiwar Ɗanmajlisar a kan ya cigaba da ayyukan alheri na gina rayuwar jama’a makamantan wannan, sannan ya buƙaci al’umma biyan kuɗin wuta a kan lokaci domin ci gaba da amfanar wutar mai ɗorewa.
“Ayyukan da Abba Bichi yake yi idan aka lura sosai wannan wakilci ne da Allah ya zaɓe shi yake yi wa al’ummarsa. Mu mutanen kirki na Bichi muna yi wa Allah godiya bisa wannan. Muna godiya a gare shi tare da fatan ya daɗe yana gudanar da irin waɗannan muhimman ayyuka amin, haka ɓangaren mutanen TCN da KEDCO dangane da haɗin kai da goyon baya da suka bayar muna godiya matuƙa da gaske.” Alhaji Garba Tukur.
Injiniya Ahmad Garko, wakilin Hukumar TCN ta ƙasa, ya ce, sun halarci taron kunna wutar ne domin shaidawa tare da jinjina ga Ɗanmajalisar bisa ayyukan taimako da yake yi, ƙarƙashin jagorancin Janar Manaja na Kano, Injiniya Alhaji Bello.
Wakilin Hukumar KEDCO, Injiniya Sabi’u Haruna, shi ma ya yaba da namijin ƙoƙarin Ɗanmajalisar, tare da nuna farin cikinsu game da gabatar da wannan muhimmin aikin ga al’umma, ya kuma ce a shirye suke wajen ba da lokacinsu ga ayyukan jama’a a duk sadda aka neme su.
“Wannan aikin wuta da aka yi in sha Allahu muna jaddada cewa za mu ci gaba da kula da layikan wutar lantarkin da aka ƙaddamar yadda yakamata. Kawai abin da za mu tunasar shi ne; idan Allah ya sa wuta ta zauna kamar yadda GM na kasuwa ya faɗa, muna fatan idan mun kawo bil ba za a samu wata matsala ba, muna kuma godiya Allah ya saka da alheri.” Injiniya Sabi’u Haruna.
Dagacin Ɗanzabuwa da ya yi magana a madadin al’ummar yankin ya ce, tun da ake samun jagorori a Ƙaramar Hukumar Bichi ba a taɓa yin nagartaccen mutum mai tausayi da tsagwaron kishi na cigaban jama’a irin Ɗanmajalisar Tarayya, Alhaji Abubakar Kabir Abubakar Bichi. Don haka sun yaba matuƙa tare da yi masa fatan alheri.






