‘Yan bindiga sun tsere sun bar dabbobi 452 da suka sace bayan musayar wuta da sojoji a Sakkwato

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Dakarun tsaro a Jihar Sakkwato sun yi nasarar daƙile wasu hare-hare biyu a ƙananan hukumomin Shagari da Rabah, lamarin da ya tilasta wa maharan sakin wasu dabbobi guda 452 da suka sace bayan musayar wuta da haɗakar tawagar jami’an tsaro.

An gudanar da atisayen ne a daren Talata wayewar Laraba, wanda ya yi sanadiyyar ƙwato ɗaruruwan dabbobi da aka sace bayan ‘yan bindigar sun tsere zuwa bayan gari.

Jami’in Hulɗa da Jama’ar rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Ahmad Rufa’i ne ya sanar da haka a wata takarda da ya fitar a ranar Alhamis.

A cewarsa, harin farko ya faru ne da misalin ƙarfe 7:20 na dare a lokacin da ‘yan bindigar suka afka wa ƙauyukan Horo Birni da Marake a Ƙaramar Hukumar Shagari, inda suka riƙa harbe-harbe kana daga bisani suka yi awon-gaba da wasu dabbobi da ba a san adadinsu ba.

Akan haka ne DPOn ‘yan sandan Shagari ya gaggauta haɗa tawagar jami’ai na musamman ciki har da ‘yan Sashen Yaƙi da Garkuwa da ‘yan ko ta kwana na ƙauyuka (VCRU) da kuma Sojojin Sansanin Forward (FOB), waɗanda suka tunkari maharan tare da yin nasarar akansu.

A nan ne aka ƙwato shanu 195 da tumaki 84 da raƙuma biyu daga hannun ‘yan bindigar, yana mai cewa ‘yan ƙauye guda biyu sun samu raunukan harbin bindiga, waɗanda tuni aka garzaya da su asibiti don ba su kulawa.

A wani atisayen kuwa, da misalin ƙarfe 8:10 na daren ne hallau ‘yan ta’adda suka kai farmaki a ƙauyen Mai-Kujera da ke Ƙaramar Hukumar Rabah, inda suka riƙa harbe-harbe tare da sace wasu dabbobin gida guda 171, ciki har da raƙuma, shanu, tumaki da awakai.

A nan ma dai kamar na Shagari, DPOn yankin ya gaggauta tura jami’an tsaro, waɗanda suka tare hanyoyin fita daga yankin, sannan suka yi musayar ruwan wuta da maharan, lamarin da ya tilasta musu tserewa tare da barin dabbobi da suka sacen.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Hayatu Hassan Shaffa ya yaba wa jami’an bisa hoɓɓasa da suka yi wajen cin galaba akan ‘yan bindigar tare jinjina musu kan ceto dukiyoyin ba tare da asarar rai ko ɗaya ba.

By Babaji