Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Babban Mai Tsawatarwa (Chief Whip) na Majalisar Wakilai, Abubakar Bwari, ya ƙalubalanci ikirarin da tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi kwanan nan kan marigayi tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Ghali Na’Abba, yana mai cewa bayanin Obasanjo game da yunƙurin tsige shi daga mulki a zamanin Jamhuriya ta Huɗu ba daidai ba ne, kuma bai yi wa marigayin adalci ba.
Bwari, wanda ya riƙe muƙamin Chief Whip tsakanin shekarar 1999 zuwa 2007, ya bayyana hakan ne a cikin wata doguwar sanarwa da ya fitar ranar Litinin mai taken “Gyara Tarihi: Martani cikin Ladabi ga Ikirarin Obasanjo kan Ghali Na’Abba.”
Sanarwar ta zo ne kwanaki kaɗan bayan Obasanjo ya mayar da martani ga wani rubutu da tsohon gwamnan Jihar Ogun, Segun Osoba, ya wallafa mai taken “Yadda Obasanjo Ya Yaudare Mu a 2003.” A cikin wasiƙarsa, Obasanjo ya yi zargin cewa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bai wa marigayi Ghali Na’Abba Naira miliyan biyar domin ya fara shirin tsige shi daga mulki.
Sai dai Bwari ya bayyana zargin a matsayin “wanda ba gaskiya ba ne kuma ba shi da adalci,” yana mai cewa ya saɓa wa tsarin kundin tsarin mulki da kuma abubuwan da suka faru a zahiri tsakanin ɓangaren zartarwa da Majalisar Dokoki a farkon Jamhuriya ta Huɗu.
Ya ce kasancewarsa cikin shugabannin Majalisar Wakilai a wancan lokaci ya ba shi cikakken sanin abin da ya faru.
“A matsayina na Chief Whip na Majalisar Wakilai a wancan lokaci, ban tsaya ina kallo ba kawai, ni na kasance a tsakiyar dukkan tattaunawar da ake yi a kullum,” in ji shi.
Bwari ya kuma tambayi yadda za a ce Naira miliyan biyar za su isa su rinjayi ‘yan majalisa su tsige shugaban ƙasa.
A cewarsa, tsige shugaban ƙasa na buƙatar samun rinjayen kuri’u biyu bisa uku na duka mambobin Majalisar Wakilai, sannan kuma Majalisar Dattawa ta bi irin wannan tsari, don haka zargin ba shi da tushe.
“Shin Baba na nufin kujerar Shugaban ƙasar Tarayyar Nijeriya darajarta Naira miliyan biyar ce?” inji Bwari.
Ya ƙara da cewa Ghali Na’Abba mutum ne mai ƙa’ida da kishin dimokuraɗiyya, wanda ba zai taɓa shiga wata yarjejeniya ta kuɗi domin tsige shugaban ƙasa ba.
Bwari ya kuma ƙaryata ikirarin Obasanjo cewa Atiku ne ke ƙarfafa yunƙurin tsige shugaban ƙasar.
A maimakon haka, ya ce Atiku shi ne babban wakilin Obasanjo da ke zuwa Majalisar Dokoki domin sasanta rikicin da ke tsakaninta da fadar shugaban ƙasa.
“Mun san Atiku ne a matsayin babban jakadan Shugaba Obasanjo, ba a matsayin wanda ke goyon bayan tsige shi ba.”
Ya ce duk lokacin da rikici ya yi ƙamari tsakanin gwamnati da Majalisar Dokoki, Atiku ne kan zo yana roƙon ‘yan majalisa su kwantar da hankalinsu.
A cewar Bwari, bayyana Atiku a matsayin wanda ya shirya makircin tsige shugaban ƙasa ya saɓa da gaskiyar siyasar lokacin.
Ya kuma ce ba kamar yadda Obasanjo ya nuna ba, ‘yan majalisar sun kai matakin fara shirin tsige shugaban ƙasar.
A cewarsa, Majalisar ta tattara laifuka masu yawa da za su iya zama hujjar tsige shugaban ƙasa, kuma da an ci gaba da shirin ne da ba don sasanci da aka yi ba.
Bwari ya tuna cewa manyan mutane da dama sun shiga tsakani domin hana rikicin ya kai ga rikicin kundin tsarin mulki tsakanin ɓangaren zartarwa da Majalisar Dokoki.
Daga cikin waɗanda ya lissafa akwai tsohon Shugaban ƙasa, Shehu Shagari; tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Yakubu Gowon; tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Aleɗ Ekwueme; dattijo Anthony Enahoro; Birgediya Abba Kyari mai ritaya; marigayi Ooni na Ife, Oba Okunade Sijuwade; marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero; da kuma tawagar gwamnoni ƙarƙashin jagorancin Segun Osoba.
Bwari ya kuma ce tsohon Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa, Abdullahi Mohammed, tare da wasu wakilan shugaban ƙasa, sun gudanar da tarurruka da dama da shugabannin Majalisar Wakilai domin nemo mafita ta siyasa.
Ya ce: “Mun shiga waɗannan tattaunawa cikin matuƙar girmama ofishin shugaban ƙasa, amma a lokaci guda muna kare ‘yancin Majalisar Dokoki.”
