Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a na Nijeriya, Alhaji Mohammed Idris, ya ce, gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da bunƙasa masana’antu, fasaha da bai wa matasa dama a matsayin ginshiƙan sauya tattalin arzikin Nijeriya ƙarƙashin shirin Renewed Hope Agenda.
Ministan ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin ƙaddamar da rangadin tawagar yaɗa labarai ta Fadar Shugaban ƙasa zuwa hedikwatar Hukumar Kula da Kimiyya da Injiniyan Kere-kere ta ƙasa (NASENI) da ke Abuja.
Idris ya ce manufofin gwamnatin Tinubu na samar da yanayi mai kyau ga masu zuba jari, bunƙasa kasuwanci da samar da ayyukan yi masu ɗorewa suna ci gaba da haifar da sakamako mai kyau.
Ya ce Renewed Hope Agenda na sauya manyan manufofin gwamnati zuwa ayyuka na zahiri, ƙirƙire-ƙirƙire, samar da guraben aikin yi da kuma damar bunƙasa tattalin arziki a faɗin Nijeriya.
Ministan ya bayyana cewa an ƙaddamar da rangadin ne domin bai wa ‘yan Nijeriya damar ganin da idanunsu yadda manufofin gwamnatin tarayya ke haifar da ci gaba a fannoni daban-daban.
Ya ce nuna gaskiya na ƙaruwa idan hukumomin gwamnati suna hulɗa kai tsaye da jama’a, yayin da ɗaukar alhaki ke ƙarfafa idan al’umma na iya tabbatar da irin ci gaban da ake samu.
Idris ya bayyana NASENI a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen bunƙasa masana’antu ta hanyar amfani da kimiyya, injiniya da fasaha, inda ya ce ayyukanta sun haɗa da ƙera kayayyaki a cikin gida, makamashi mai sabuntawa, inganta noma, fasahar zamani da horar da matasa.
Ya ƙara da cewa burin Shugaba Tinubu shi ne gina tattalin arziki mai dogaro da ƙirƙire-ƙirƙire, ƙara darajar kayayyakin cikin gida da kuma ƙarfafa gasa a fannin masana’antu.
A cewarsa, manufar gwamnati ita ce sauya Nijeriya daga ƙasar da ta fi amfani da kayayyakin waje zuwa ƙasar da ke ƙerawa, ƙirƙire-ƙirƙire da kuma fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen duniya.
Ministan ya yabawa shugabanci da ma’aikatan NASENI bisa ƙoƙarin da suke yi wajen bunƙasa fasahar cikin gida da rage dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ƙasashen waje.
Ya kuma yaba wa mambobin tawagar yaɗa labaran Fadar Shugaban ƙasa saboda rawar da suke takawa wajen isar da sahihan bayanai ga al’umma kan ayyuka da shirye-shiryen gwamnatin tarayya.
Tun da farko, Shugaban Hukumar NASENI, Khalil Halilu, ya ce hukumar na aiwatar da tsare-tsaren bunƙasa masana’antu da suka mayar da hankali kan ƙera kayayyaki a cikin gida, musayar fasaha, ƙirƙire-ƙirƙire a fannin lafiya da kuma mayar da bincike zuwa kasuwanci.
Halilu ya ce ayyukan NASENI sun mamaye manyan fannoni takwas na masana’antu, tare da aiwatar da ayyuka a shiyyoyi shida na ƙasar da kuma Babban Birnin Tarayya, Abuja.
Ya ce manufar hukumar ita ce gina masana’antu masu ɗorewa ta hanyar ƙera kayayyaki da suka dace da kasuwar Nijeriya, haɗa su a cikin gida, ƙara amfani da kayan cikin gida da kuma kafa masana’antun da za su iya yin gogayya a kasuwannin duniya, inji shi.
