Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Nijeriya ta samu kimanin Naira tiriliyan 24.02 daga fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje a watanni shida na farkon shekarar 2026, bayan da ta fitar da ganga miliyan 182.2 na ɗanyen mai.
Hakan ya samu ne sakamakon tashin farashin mai a kasuwannin duniya, duk da ci gaba da nuna damuwa kan wadatar ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
Binciken alƙaluman samar da ɗanyen mai da fitar da shi tsakanin watan Janairu zuwa Yuni ya nuna cewa darajar gangunan man da aka fitar ta kai kusan dala biliyan 17.6, bisa canjin kuɗi na Naira 1,365 kan kowace dala.
Bayanan da aka samo daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) sun nuna cewa a wannan lokaci, Nijeriya ta samar da kimanin ganga miliyan 263.65 na ɗanyen mai, wanda darajarsa ta kai kusan dala biliyan 25.41, kwatankwacin Naira tiriliyan 34.69.
Alƙaluman sun nuna cewa kusan kashi 69 cikin 100 na ɗanyen man da wasar ta samar an fitar da shi zuwa ƙasashen waje, yayin da kusan ganga miliyan 81.45 suka rage domin tacewa a cikin gida, gudanar da ayyukan masana’antu, adanawa da sauran buƙatun fasaha.
Rahoton ya nuna cewa yawan ɗanyen man da aka samar ya riƙa sauyawa a cikin watannin shida. An samar da ganga miliyan 45.26 a watan Janairu, kafin adadin ya ragu zuwa ganga miliyan 36.68 a watan Fabrairu. Daga nan kuma ya ci gaba da ƙaruwa har ya kai ganga miliyan 47.43 a watan Mayu, yayin da aka kiyasta samar da ganga miliyan 46.8 a watan Yuni.
Haka kuma, yawan ɗanyen man da aka fitar ya ƙaru daga ganga miliyan 24.08 a watan Fabrairu zuwa ganga miliyan 33.48 a watan Mayu, sannan ya tsaya a kusan ganga miliyan 33.3 a watan Yuni.
Rahoton ya bayyana cewa hauhawar kuɗaɗen da Najeriya ta samu daga fitar da mai ba wai saboda ƙarin yawan man da aka samar ba ne, illa dai tashin farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.
Farashin mai ya yi tashin gwauron zabo tsakanin watan Maris da Mayu sakamakon rikice-rikicen siyasa a Gabas ta Tsakiya da kuma matsalolin zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Strait of Hormuz. Ko a watan Yuni ma, farashin ya ci gaba da kasancewa sama da yadda yake a farkon shekarar.
Sai dai duk da wannan nasara da aka samu wajen fitar da mai, har yanzu ana ci gaba da nuna damuwa kan wadatar ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
Masana a harkar man fetur sun sha bayyana cewa kamfanonin da ke hako ɗanyen mai sun fi karkata wajen fitar da shi ƙasashen waje saboda yawan ribar da ake samu, duk da tanadin da ke cikin Dokar Masana’antar Man Fetur, wadda ta wajabta samar da isasshen ɗanyen mai ga matatun cikin gida.
Wannan batu ne ya jawo takun-saƙa tsakanin Matatar Dangote da Gwamnatin Tarayya. Matatar ta zargi gwamnati da hukumominta da gaza tabbatar da isasshen ɗanyen mai domin gudanar da ayyukanta.
Matatar ta kai ƙarar gwamnati kotu, tana mai cewa ƙarancin ɗanyen man da ake ware mata ya yi tasiri ga ayyukanta. Sai dai Gwamnatin Tarayya ta musanta wannan zargi.
A nata ɓangaren, ƙungiyar Masu Mallakar Matatun ɗanyen Mai ta Nijeriya ta buƙaci gwamnati da ta tabbatar da cikakken aiwatar da dokar samar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida, tana mai cewa hakan zai tabbatar da wadatar ɗanyen mai ga matatun cikin gida tare da ci gaba da kare kuɗaɗen shiga da ƙasar ke samu daga fitar da mai.
