Iyalan Marigayi Baba A.T sun roƙi gwamnatin Kebbi ta biya bashin kwangilar da ake bin sa

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Iyalan Marigayi Malam Aliyu S. Abubakar Tunga (Baba A.T.) sun yi kira ga Gwamnatin Jihar Kebbi da ta biya kuɗaɗen kwangilar da ake bin marigayin domin su samu damar biyan bashin da ya bari.

Da yake zantawa da wakilin Blueprint Manhaja a ranar Litinin, Malam Aminu Aliyu Abubakar Tunga, wanda ya yi magana a madadin iyalan marigayin, ya bayyana cewa shekaru shida kenan da rasuwar mahaifinsu, amma har yanzu ba su samu damar biyan bashin da ya bari ba saboda gwamnatin jihar ba ta biya kuɗaɗen kwangilar da ake binsa ba.

A cewarsa, marigayin na bin Gwamnatin Jihar Kebbi kuɗaɗen kwangilar ciyar da ɗaliban Goɓernment Secondary School (GSC) Dakingari, wadda aka aiwatar tun lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Sa’idu Usman Dakingari.

Ya yi kira ga Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris (Kauran Gwandu), da ya duba batun tare da tabbatar da biyan duk wani haƙƙin da gwamnati ke bin marigayin ko kuma warware duk wani abin da ya shafi wannan bashi.

Aminu ya bayyana cewa marigayin ya shafe shekaru yana bibiyar kuɗaɗen nasa, har zuwa lokacin gwamnatin tsohon Gwamna Atiku Bagudu, amma bai samu nasarar karɓarsu ba kafin rashin lafiyarsa ta tsananta, daga bisani ya rasu a ranar 2 ga Agusta, 2020.

Ya ƙara da cewa marigayin ya taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ilimi da tarbiyyar ɗalibai a Jihar Kebbi, inda ya horas da ɗalibai da dama waɗanda a yau suka samu ci gaba a rayuwarsu.

Saboda haka, ya yi kira ga tsofaffin ɗaliban marigayin, musamman waɗanda ke da tasiri a cikin al’umma da kuma masu kusanci da gwamnatin jihar, da su taimaka wajen isar da wannan buƙata ga Gwamna Nasir Idris, wanda shi ma malami ne, domin a tabbatar an biya haƙƙin marigayin.

By ukarofi

Leave a Reply