Atiku ga Obasanjo: Na zaɓi Nijeriya da dimokuraɗiyya fiye da biyayya ga wani

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya mayar da martani ga tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, inda ya ce bai taɓa yin nadamar adawa da yunƙurin wa’adin mulki na uku ba, yana mai jaddada cewa ya zaɓi kare Nijeriya da dimokuraɗiyya fiye da biyayya ga mutum.

Atiku, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC a zaɓen 2027, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Phrank Shaibu, ya fitar.

Martanin na Atiku ya biyo bayan kalaman da Obasanjo ya yi, inda ya bayyana cewa zaɓen Atiku a matsayin mataimakinsa a zaɓen 1999 shi ne babban kuskuren siyasa da ya taɓa yi.

Atiku ya ce ya karɓi kalaman tsohon shugaban ƙasar da baƙin ciki, ba da fushi ba, yana mai cewa sun nuna yadda ƙiyayya ta kashin kai ta rinjayi yadda Obasanjo ke kallon tarihin mulkinsu.

Ya ce tushen saɓanin da ke tsakaninsu shi ne yadda ya ƙi mara wa yunƙurin gyaran kundin tsarin mulki domin bai wa Obasanjo damar yin wa’adi na uku baya.

“Ina alfahari da cewa na tsaya tsayin daka wajen hana wa’adin mulki na uku. Na tsaya tare da Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya, kuma ba ni da wani nadama kan hana duk wani yunƙuri na rusa dimokuraɗiyyarmu saboda muradin mutum.”

Atiku ya ƙara da cewa idan ƙiyayyar Obasanjo a kansa ta samo asali ne saboda matsayinsa kan wa’adin mulki na uku, to yana ɗaukar hakan a matsayin abin alfahari.

Ya ce babu wani mutum da ya fi Tarayyar Nijeriya girma, yana mai jaddada cewa Kundin Tsarin Mulki shi ne mafi girma.

Atiku ya bayyana cewa rikicin da ya shiga da Obasanjo ba rikici ne na kashin kai ba, illa yaƙi ne domin kare dimokuraɗiyya da tabbatar da bin kundin tsarin mulki.

A cewarsa, al’ummar Nijeriya ne suka yi nasara a wannan gwagwarmaya, kuma tarihi ya riga ya yanke hukunci.

Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya kuma yi watsi da duk wani yunƙuri na rage irin gudunmawar da ya bayar wajen nasarorin tattalin arzikin gwamnatin Obasanjo.

Ya yi nuni da cewa Darakta Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, ta yaba wa ƙungiyar kula da tattalin arziki da ya jagoranta lokacin yana mataimakin shugaban ƙasa.

Atiku ya ce abin mamaki ne yadda wasu manyan mutane ke yaba masa kan irin rawar da ya taka, amma Obasanjo na ƙoƙarin rage darajar wannan gudunmawa.

Ya kuma tuna cewa lokacin da Obasanjo ke tsare a gidan yari a zamanin mulkin Janar Sani Abacha, ya tsaya masa tsayin daka tare da tallafa wa iyalansa, sannan ya yi aiki tare da wasu domin ganin an sake shi.

A cewarsa, bayan fitowar Obasanjo daga gidan yari, ya taimaka masa ta fuskar siyasa da rayuwa, har ma ya haɗa ƙawance da tsarin siyasa da suka kai ga nasararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 1999.

Sai dai ya ce bai taɓa yin nadamar wannan taimako ba, domin yana ganin taimakon mutane ibada ce, ba kasuwanci ba.

Atiku ya kuma yi kira ga Obasanjo da sauran shugabanni da su maida hankali kan matsalolin da Nijeriya ke fuskanta, kamar tsadar rayuwa, rashin tsaro, rashin aikin yi da kuma farfaɗo da tattalin arziki, maimakon sake buɗe tsofaffin rigingimun siyasa.

Ya jaddada cewa ya daɗe yana ƙin mayar da martani ga kalaman Obasanjo saboda girmama ofishin shugaban ƙasa da kuma irin dangantakar da suka taɓa yi, amma ya ce ba zai ci gaba da yin shiru ba idan ana ƙoƙarin karkatar da tarihin abin da ya faru.

A ƙarshe, Atiku ya ce Obasanjo na da ‘yancin bayyana ra’ayinsa, amma ba shi da ikon sauya gaskiyar tarihi, yana mai cewa tarihin siyasar Nijeriya zai tabbatar da irin gudunmawar da ya bayar wajen kare dimokuraɗiyya da kuma gina ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply