Gwamnan Zamfara ya jinjina wa Shugaban APC na Ƙasa kan jagorancinsa yayin cika shekara 58

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya miƙa saƙonsa na taya murna ga Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda bisa zagayowar ranar haihuwarsa ta cikar sa shekaru 58 a duniya, yana mai yaba wa jagoranci da gudunmawarsa ga ci-gaban jam’iyyar.

A ranar Asabar, 8 ga Agusta, 2026 ne farfesan ya cika shekara 58 a duniya, inda gwamnan Zamfarar ya bayyana shi a matsayin muhimmin jigo acikin APC kuma mai taka muhimmiyar rawa ga ci-gaban harkokin siyasa a Nijeriya.

A saƙonsa na taya murna ga Yilwatda, Dauda Lawal ya kuma ce a matsayinsa na ƙwararre ta fuskar ilimi kuma jajirtaccen jagoran jam’iyya, farfesan yana fifita ci-gaban APC acikin lamuran siyasa, lamarin da ke taimaka wa harkokin tafiyar da ita bisa tsari da shugabanci na gari.

Haka kuma, ya jinjina wa jagoranci da hangen nesansa , waɗanda suna taimaka wa muhimman shirye-shirye da ƙarfafa haɗin kai acikin ‘ya’yan jam’iyyar tare da kauce wa dukkan wata hanya da za ta kai ga rarrabuwar kai.

Gwamna Lawal ya kuma yaba da yadda shugaban APCn ya jagoranci zaɓukan fidda gwanin jam’iyyar na kwanan nan, yana mai cewa dattakonsa ya nuna cewa akwai ilimi, horo, gaskiya da jajircewa akan abin yake na daidai a tare da shi.

Kazalika, ya yi wa Farfesa Yilwatda addu’ar fatan cigaba da kasancewa lafiyayye da kuma samun shekaru masu albarka a nan gaba wajen hidimta wa APC da ma ƙasa baki ɗaya.

By Babaji