Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Mataimakin Shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima, ya yi kira ga masu zuba jari daga ƙasar Saudiyya da su yi amfani da ɗimbin damar kasuwanci da ke Nijeriya, yana mai tabbatar musu cewa Gwamnatin Tarayya ta samar da yanayi mai kyau da zai ba su damar gudanar da harkokinsu cikin kwanciyar hankali.
Shettima ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin buɗe baje kolin zuba jari da yawon buɗe ido na Nijeriya da Saudiyya na kwanaki biyu da aka gudanar a Abuja. Kamfanin Al-Yaro International Limited ne ya shirya taron tare da haɗin gwiwar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna ƙasashen Waje (NiDCOM).
Mataimakin shugaban ƙasar, wanda Mataimaki na Musamman ga Shugaban ƙasa kan Faɗaɗa Fitar da Kayayyaki Zuwa ƙasashen Waje, Aliyu Bunu Sheriff, ya wakilta, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na mai ba, da samar da yanayi mai jan hankalin masu zuba jari daga sassa daban-daban na duniya, cikin manyan manufofinta.
Ya ce Nijeriya da Saudiyya na da babbar dama ta ƙarfafa alaƙar tattalin arziki, musamman ta fuskar faɗaɗa kasuwanci da kuma cin gajiyar kasuwar halal ta duniya, wadda ke ci gaba da bunƙasa.
“Nijeriya a buɗe take, kuma a shirye take domin karɓar masu zuba jari. A ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, gwamnati ta bai wa bunƙasa fitar da kayayyakin da ba na mai ba da kuma inganta yanayin kasuwanci muhimmanci na musamman,” inji shi.
Shettima ya ce lokacin gudanar da baje kolin ya dace matuƙa, domin ƙasashen biyu na neman ƙara haɗin gwiwa a fannoni kamar noma, yawon buɗe ido, lafiya, makamashi, gine-ginen more rayuwa, sufuri da fasaha.
Ya buƙaci masu zuba jari daga Saudiyya su daina kallon Nijeriya a matsayin kasuwar cikin gida kawai, yana mai cewa ita ce mafi girman tattalin arziki a Afirka, kuma tana da damar shiga kasuwar Yarjejeniyar Ciniki Cikin Nahiyar Afirka (AfCFTA) mai masu amfani da sama da biliyan ɗaya.
A cewarsa, ƙarin jarin da Saudiyya za ta kawo Nijeriya zai ƙara ƙarfafa alaƙar tattalin arzikin ƙasashen biyu tare da samar da sabbin damammaki ga ’yan kasuwa. Ya kuma bayyana cewa Saudiyya ba ƙasa ce mai arziki kaɗai ba, domin sauye-sauyen da take aiwatarwa ƙarƙashin shirin Vision 2030 sun mayar da ita ɗaya daga cikin ƙasashen da tattalin arziƙinsu ke bunƙasa cikin sauri.
Aliyu Bunu Sheriff ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na aiwatar da sabon tsarin tattalin arzikin halal, da nufin mayar da Nijeriya cibiyar kasuwar halal mafi girma a Afirka. Ya ce kasuwar halal ta duniya ta haura darajar dala tiriliyan bakwai, kuma wannan zai buɗe ƙofofin zuba jari a fannoni kamar noma, kiwon dabbobi, sarrafa abinci, magunguna, kayan kwalliya, harkokin sufuri da kuma harkokin kuɗaɗen Musulunci. A cewarsa, Saudiyya na daga cikin manyan abokan hulɗar Nijeriya wajen tsara wannan shiri.
Ya ƙara da cewa Nijeriya na da fa’idoji da suka haɗa da yawan jama’a, albarkatun noma da dabbobi, matasa masu ƙwazo da kuma kusanci da kasuwannin ƙasashen Larabawa, wanda hakan ke ƙara jan hankalin masu zuba jari.
Shettima ya yabawa NiDCOM da Al-Yaro International Limited bisa samar da dandalin da ke ƙarfafa alaƙa tsakanin al’ummomi da kuma bunƙasa kasuwanci tsakanin Nijeriya da Saudiyya. Ya kuma tabbatar wa mahalarta taron cewa gwamnatin tarayya za ta yi aiki tare da duk wani mai zuba jari mai niyya domin tabbatar da cewa tattaunawar da aka fara za ta koma yarjejeniyoyi da kuma manyan ayyukan zuba jari.
A nata jawabin, Shugaba kuma Babbar Daraktar Hukumar ’Yan Nijeriya Mazauna ƙasashen Waje (NiDCOM), Dakta Abike Dabiri-Erewa, ta yi kira da a kafa kamfanonin haɗin gwiwa tsakanin Nijeriya da Saudiyya domin bunƙasa tattalin arzikin ƙasashen biyu. Ta ce ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ba kuɗin da suke aikowa gida kaɗai suke bayarwa ba, suna kuma kawo ƙwarewa, sabbin dabaru da haɗin gwiwar kasuwanci da ke taimaka wa ci gaban ƙasa.
Dabiri-Erewa ta bayyana cewa Saudiyya na ɗaya daga cikin ƙasashen Gabas ta Tsakiya da ke da ɗimbin ’yan Nijeriya ƙwararru, ciki har da likitoci, injiniyoyi da ’yan kasuwa, waɗanda ke ba da gudunmawa sosai ga tattalin arzikin ƙasar. Ta yi ƙorafin cewa ana yawan ɗaukar hoton ’yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ta mummunar fuska, alhali mafi yawansu mutane ne masu ƙwazo da ke wakiltar ƙasar cikin mutunci.
A cewarta, baje kolin zai ƙarfafa alaƙar kasuwanci tsakanin kamfanonin ƙasashen biyu a fannoni kamar makamashi, gine-ginen more rayuwa, otel-otel, sufuri, fasaha, lafiya da yawon buɗe ido.
Da take magana da manema labarai bayan taron, Dabiri-Erewa ta ce baje kolin ya nuna ƙarara cewa Nijeriya ta shirya karɓar masu zuba jari. Ta bayyana cewa ’yan Nijeriya da ke zaune a Saudiyya ne suka taka muhimmiyar rawa wajen haɗa masu zuba jari daga ƙasar da Nijeriya, tare da ƙarfafa kamfanonin Nijeriya su faɗaɗa kasuwancinsu zuwa Saudiyya.
Ta nuna fatan cewa haɗin gwiwar da aka fara a wajen taron zai haifar da sabbin jarin da za su samar da ayyukan yi, ƙara fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje da kuma ƙarfafa alaƙar tattalin arziƙi tsakanin Nijeriya da Saudiyya.
