
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanata Francis Fadahunsi da ke wakiltar mazaɓar Osun ta Gabas a Majalisar Dattawan Nijeriya ya yi bayanin ainihin abin da kalamarsa ta “kill Accord” take nufi, inda ya ce yana nufin a yi galaba akan jam’iyyar a zaɓen gwamnan jihar da ke tafe ba wai a farmaki mambobinta ba kamar yadda wasu suka ɗauka.
Wannan warwara na zuwa ne a daidai lokacin da Rundunar ‘Yan sanda ta tabbatar da kisan mutane uku a wani rikicin ‘yan ƙungiyar asiri da ya gudana a garin Ilesa da ke jihar, kwanaki kaɗan kafin zaɓen gwamnan jihar da za a gudanar a ranar 15 ga Agusta.
Fadahunsi na fuskantar suka ne bayan ganin sa a wani faifai bidiyo da ya karaɗe kafafen sada zumunta, inda yake yi wa magoya bayan Jam’iyyar APC jawabi a garin Ilesa.
An zargi sanatan da faɗa wa magoya bayan nasa da su “halaka” mambobin jam’iyyar AP, waɗanda aka gani a yankin kafin ko a ranar zaɓen.
Saidai, a wata sanarwa da ofishin yaɗa labaransa ya fitar wadda aka yi wa laƙabi da “Kill Osun Accord Votes, Not Violence”, Fadahunsi ya ce kalaman nasa siyasa ne kuma zaurance.
A cewar sanarwar, Sanata Fadahunsi bai yi kira ga a tayar da hankali, wulaƙanci ko kai farmaki akan mamban AP ko magoya bayanta ba ko ma akan wata jam’iyya ta daban. Sanata ya bayyana cewa, manufarsa ita ce na yin kira ga magoya bayan APC su yi galaba akan Accord Party ta hanyar kaɗa ƙuri’unsu yayin zaɓen.
Baya ga haka, sanatan ya yi kira ga hukumomin tsaro da su cigaba da kasancewa masu aiki bisa ƙwarewa da tabbatar da masu zaɓe sun yi amfani da damar da suka samu na ‘yancin da dokar ƙasa ta ba su ba tare da wata fargaba ba ko cin mutunci ba.
