Tare da BILKISU YUSUF ALI, Ph’D
Gabatarwa:
Tsaftar muhalli na da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da lafiyar dabbobi da haɓaka yawan amfanin kiwo. ƙazantar wurin kiwo na haifar da taruwar ƙwayoyin cuta da ƙwari da gurɓataccen ruwa, waɗanda ke haddasa cututtuka da rage ƙarfin dabbobi da ingancinsu. Duk lokacin da aka bar wurin kiwo da ƙazanta ba tare da kula ba to tabbas waɗannan matsalolin ne za su faru.
1. Yaɗuwar cututtukan ƙwayoyin cuta
Taruwar kashin dabbobi da fitsari na samar da muhalli mai kyau ga ƙwayoyin cuta irin su Salmonella, Escherichia coli (E. coli) da Clostridium. Waɗannan ƙwayoyin cuta na iya jawo gudawa da zazzabi da rashin cin abinci da mutuwar dabbobi, musamman ƙanana.
2. Yawaitar kwari da kwari
ƙazantar wurin kiwo na jawo ƙudaje da sauro da kaska. Waɗannan na iya yaɗa cututtuka daga dabba zuwa dabba, su kuma haddasa ciwon fata, raunuka da rage lafiyar dabbobi.
3. Cututtukan ƙafafu
Idan dabbobi suna yawan tafiya a cikin laka da kashi, ƙafafunsu kan kamu da ciwo, su kumbura ko su ruɓe. Wannan na sa su yi wahalar tafiya, su rage cin abinci kuma nauyinsu ya ragu.
4. Cututtukan numfashi
Rashin tsafta da wari daga fitsari da kashin dabbobi na ƙara iskar ammonia a cikin rumfa. Idan wannan iska ta yi yawa, tana iya jawo tari, wahalar numfashi da kumburin hanyoyin numfashi.
5. Rage samar da madara da nama
Dabbobin da ke fama da cututtuka ko damuwa saboda muhalli mai ƙazanta sukan rage cin abinci. Hakan yana rage yawan madara, saurin girma da ingancin nama, wanda ke jawo asarar tattalin arziƙi ga mai kiwo.
6. Matsalolin haihuwa
Muhalli mai ƙazanta na iya ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan mahaifa bayan haihuwa, zubar da ciki, jinkirin ɗaukar ciki da haihuwar ‘ya’ya marasa ƙarfi.
7. Yawaitar tsutsotsi
ƙazantar wurin kiwo da gurɓataccen ciyawa ko ruwa na taimakawa wajen yaɗuwar ƙwayayen tsutsotsi. Idan dabbobi suka kamu, suna ramewa, jin rauni da rage yawan amfanin kiwo.
Hanyoyin rigakafi
Tsaftace kashi da fitsari kullum.
Samar da magudanar ruwa domin kada ruwa ya tsaya.
Wanke wuraren kiwo da sinadaran kashe ƙwayoyin cuta akai-akai.
Samar da iska mai kyau a rumfunan dabbobi.
Killace dabbar da ta kamu da cuta.
Yin allurar rigakafi da ba da maganin tsutsotsi bisa shawarar likitan dabbobi.
Samar da ruwa da abinci masu tsafta.
Kammalawa:
Muhalli mai tsafta yana rage yaɗuwar cututtuka, yana inganta lafiyar dabbobi da ƙara yawan amfanin kiwo. Saboda haka, tsaftar wurin kiwo ba kawai kariya ce ga lafiyar mutane ba, har ma hanya ce ta bunƙasa kiwon dabbobi da rage asarar tattalin arziki.
