Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wata mata da ’yan bindiga suka tilasta wa barin gidanta a ƙaramar Hukumar Tambuwal ta Jihar Sakkwato, ta bayyana irin mummunan halin da ta shiga, inda ta ce ta haifi jaririnta a kan hanya yayin da take tserewa daga hare-haren ’yan bindiga da suka mamaye garinsu tare da ƙona gidaje.
Matar ta bayyana haka ne cikin harshen Hausa yayin wata tattaunawa da Iconic FM, inda ta ce hare-haren sun lalata dukiyoyin iyalansu, har ta kai ga ba ta da isasshen kayan da za ta yi amfani da su wajen ɗaukar jaririn da ta haifa.
A cewarta, ’yan bindigar sun shiga garinsu, suka kwashe kekuna da sauran kayayyaki, suka kashe kaji tare da lalata dukiyoyin jama’a, kafin daga bisani su tilasta musu barin gidajensu.
Ta ce, hare-haren sun kuma daƙile harkar noma, wadda ita ce babbar hanyar samun abin dogaro ga mafi yawan mazauna yankunan da lamarin ya shafa.
“Yayin da lokacin noma ya zo, suka hana mu zuwa gonakinmu. Yanzu sun hana mu noma, sun ƙona garinmu, sun kai mana hari, sannan suka jefa mu cikin wannan hali,” inji ta.
Matar ta ce tsananin halin da suke ciki ya kai matakin da mutanen da aka raba da muhallansu ba sa iya komawa gidajensu cikin aminci.
Ta bayyana cewa ’yan bindigar kan mamaye wasu garuruwa da dazuzzukan da ke kewaye da su na tsawon lokaci, lamarin da ke hana mazauna yankunan komawa gidajensu da gonakinsu. Ta kuma koka kan wahalar samun kulawar lafiya, inda ta ce wasu iyalai da aka raba da muhallansu kan fuskanci matsala wajen samun magani, har ma ana buƙatar su biya kuɗi kafin a kula da su.
“Komai ya zama wahala. Ko lokacin da nake cikin irin wannan ƙunci, na haifi jaririna a kan hanya. Ba su bar ni da isasshen zani da zan ɗauki jaririn ba.
“Ka sani, idan wahala ta yi tsanani, mace mai juna biyu za ta iya haihuwa a kan hanya,” inji ta.
Matar na daga cikin mutanen da sabbin hare-haren ’yan bindiga suka raba da muhallansu a wasu yankunan ƙananan hukumomin Shagari da Tambuwal na Jihar Sakkwato.
Bayan shafe sama da watanni uku suna gudun hijira, sabbin hare-haren sun sake tilasta wa wasu mazauna garuruwa barin gidajensu, inda suka nemi mafaka a Jabo. Wasu na zaune a wurin ’yan uwansu, yayin da wasu kuma aka ba su matsuguni a wata makarantar firamare.
Magaji Abdullahi, wani daga cikin mutanen da aka raba da muhallansu da ke zaune a makarantar, ya ce ’yan bindigar sun kwashe kusan dukkanin abin da al’ummarsu ta mallaka. Ya ce sun bar gidajensu ne saboda hare-haren ’yan bindiga, suka zo Jabo domin neman mafaka da zaman lafiya.
A cewarsa, ’yan bindigar sun kashe wasu mazauna yankin tare da kwashe shanu, jakuna, awaki da kaji. Ya ce matsalar rashin tsaro ta shafe shekaru tana ci gaba, amma a bana lamarin ya ƙara tsananta, inda mutane suka kasa yin noma, kiwon dabbobi ko kamun kifi.
“Babu noma, babu kiwon dabbobi, babu kamun kifi, babu kuma wata hanyar samun abin dogaro kamar da,” inji shi.
Abdullahi ya roƙi gwamnati da ta dawo da zaman lafiya tare da samar da abinci da sauran muhimman buƙatu ga mutanen da aka raba da muhallansu. Ya ce, a halin yanzu wasu ƙananan tallafe-tallafe daga mutane ne kawai suke taimaka musu, inda suke amfani da kuɗin wajen sayen masara da suke ci.
Shaidun mutanen da aka raba da muhallansu sun nuna yadda matsalar rashin tsaro da ta daɗe tana addabar wasu yankunan kudancin Sakkwato ta wuce kashe-kashen rayuka kawai, inda ta durƙusar da noma, kiwo, kamun kifi, harkokin lafiya, rayuwar iyali da kuma samun abinci.
Yankunan Tambuwal da Shagari, da wasu sassan Budinga da Tureta, na ci gaba da fuskantar matsalolin tsaro, lamarin da ya hana dubban mazauna yankunan komawa gidajensu.
Ga matar da ta haifi jaririnta a kan hanya, hare-haren ’yan bindigar sun mayar da abin da ya kamata ya kasance lokacin farin ciki da haihuwar ɗa zuwa wani mummunan sakamakon rikicin da ya kwace wa dubban ’yan Nijeriya tsaro, hanyar samun abin dogaro da kuma mutuncin rayuwa.
