Zaɓen Osun: Sufeto Janar ya tura DIG Ishyaku domin jagorantar tsaro

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Sufeto Janar na ’Yan Sandan Nijeriya, IGP Olatunji Disu, ya tura Muƙaddashin Babban Sufeto Janar, DIG Ishyaku Mohammed, zuwa Jihar Osun, domin jagorantar daidaita ayyukan tsaro yayin zaɓen gwamnan njihar da za a gudanar ranar Asabar, 15 ga Agusta, 2026.

A cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya (FPRO), CSP Anietie Iniedu, ya fitar a Abuja, ya ce tura babban jami’in na daga cikin matakan da rundunar ta ɗauka domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin zaman lafiya, tsaro da sahihanci a faɗin jihar.

Ya ce, DIG Ishyaku Mohammed ne zai jagoranci ɓangaren ayyukan ’yan sanda na tsarin tsaron zaɓen, tare da yin aiki kafaɗa da kafaɗa da sauran hukumomin tsaro ƙarƙashin Kwamitin Tuntuɓar Hukumomin Tsaro Kan Zaɓe (ICCES).

Sanarwar ta ce Mataimakan Sufeto Janar na ’Yan Sanda da Kwamishinonin ’Yan Sanda da aka tura zuwa gundumomin sanata uku na jihar za su mara masa baya wajen sa ido kan ayyukan tsaro, ƙarfafa tattara bayanan sirri da kuma tabbatar da gaggawar tunkarar duk wata barazana da ka iya tasowa.

CSP Iniedu ya ce rundunar ta tanadi isassun matakan tsaro domin kare masu kaɗa ƙuri’a, jami’an Hukumar Zaɓe ta ƙasa (INEC), kayan zaɓe, rumfunan zaɓe, cibiyoyin tattara sakamako, masu sa ido da aka amince da su da kuma ’yan jarida, kafin, lokacin da kuma bayan zaɓen.

IGP Disu ya kuma gargaɗi ’yan siyasa, magoya bayansu da duk wani mai shirin tayar da tarzoma cewa za a kama tare da gurfanar da duk wanda aka samu da hannu wajen satar akwatin ƙuri’a, tsoratar da masu kaɗa ƙuri’a, daba da sauran laifukan zaɓe.

Rundunar ta kuma sake jaddada haramcin rakiyar ’yan siyasa ko manyan baƙi zuwa rumfunan zaɓe ko cibiyoyin tattara sakamako da masu ɗauke da makamai, jami’an tsaro na kansu ko wasu mutanen da ba su da izinin yin irin wannan aiki.

Haka kuma, rundunar ta hana ƙungiyoyin tsaro da gwamnatocin jihohi suka kafa, ƙungiyoyin tsaro na sa-kai da sauran ƙungiyoyin tsaro masu zaman kansu shiga aikin tsaron zaɓen, bisa tanade-tanaden da rundunar ’yan sandan ta gindaya.

Rundunar ta ce, ta gamsu da irin matakan da aka ɗauka domin tabbatar da tsaron jihar, tare da kira ga mazauna Osun, masu kaɗa ƙuri’a da baƙi da su kwantar da hankulansu.

Ta kuma buƙaci dukkan waɗanda suka cancanci kaɗa ƙuri’a su fito su yi amfani da ’yancinsu cikin zaman lafiya ba tare da tsoro ko barazana ba. Rundunar ’yan sandan ta sake tabbatar da aniyarta ta gudanar da aikinta cikin ƙwarewa, tsaka-tsaki, mutunta haƙƙin ɗan Adam da kuma kare tsarin zaɓe.

By ukarofi

Leave a Reply