Chadi za ta bai wa ƙasashen Afirka izinin shiga ƙasar babu biza

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Jamhuriyar Chadi ta sanar da cewa daga 1 ga Janairu, 2027, ’yan ƙasa daga dukkan ƙasashen Afirka za su samu damar shiga ƙasar ba tare da neman takardar izinin shiga ƙasa, wato biza, ba.

Shugaban ƙasar Chadi, Mahamat Idriss Deby, ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin ƙasar na ƙarfafa haɗin kan Afirka da kuma sauƙaƙa zirga-zirgar mutane da kayayyaki tsakanin ƙasashen nahiyar.

Deby ya bayyana cewa cire takunkumin biza zai taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin ƙasashen Afirka, tare da sauƙaƙa tafiye-tafiye daga wata ƙasa zuwa wata.

A cewarsa, wannan manufa ta nuna yadda Chadi ke da ƙudurin mara wa babban burin haɗin kan Afirka da haɗewar tattalin arzikin yankuna baya.

Ana kuma sa ran matakin zai sauƙaƙa wa ’yan yawon buɗe ido, ’yan kasuwa da sauran ’yan Afirka shiga Chadi, wadda ke yankin Afirka ta Tsakiya.

Da wannan sanarwa, Chadi ta zama ƙasa ta takwas a Afirka da aka ruwaito ta ɗauki tsarin bai wa ’yan ƙasashen Afirka damar shiga ba tare da biza ba.

Sauran ƙasashen da suka ɗauki irin wannan mataki sun haɗa da Jamhuriyar Benin, Gambia, Rwanda, Seychelles, Ghana, Kenya da Togo.

A watan Mayun da ya gabata ne Togo ta sanar da cewa ’yan ƙasashen Afirka masu ingantattun fasfo za su iya shiga ƙasar ba tare da neman biza ba.

By ukarofi

Leave a Reply