Kotun Syria ta yanke wa tsohon shugaban ƙasar Bashar Assad hukuncin kisa

Spread the love

Kotun hukunta manyan laifuka da ke Damascus, babban birnin Syria, ta yanke wa tsohon shugaban kasar, Bashar al-Assad, hukuncin kisa kan laifukan da aka danganta da yaƙin basasar ƙasar.

Kotun ta same shi da laifin kisan gilla da aka shirya tun da wuri, tare da ɗora masa alhakin amfani da hukumomin gwamnati wajen aikata laifukan yaƙi da laifukan cin zarafin bil’adama.

An yanke hukuncin ne ba tare da Assad ya halarta ba, domin tun bayan kifar da gwamnatinsa a watan Disambar 2024 ya tsere zuwa Rasha, inda ya samu mafaka.

Hukuncin ya kasance na musamman a tarihin Syria bayan faɗuwar gwamnatin Assad, domin shi ne karon farko da tsohon shugaban ƙasar ko wani babban mutum daga cikin makusantansa ya fuskanci hukunci daga kotunan ƙasar kan laifukan da aka aikata a lokacin mulkinsa.

Alƙalin da ya jagoranci zaman, Fakhareddine al-Aryan, ya bayyana cewa gwamnatin Assad ta yi amfani da hukumomin ƙasar wajen aikata laifukan yaƙi da kuma laifukan cin zarafin bil’adama.

An kuma yanke wa ɗan uwan Assad, Atef Najib, hukuncin kisa. Najib, wanda ya taɓa jagorantar sashen tsaron siyasa a lardin Deraa da ke kudancin Syria, shi ne mutum mafi girma daga cikin tsoffin jami’an gwamnatin Assad da ya bayyana a gaban kotu a wannan shari’a.

Najib ya fuskanci zargin kisan gilla da azabtarwa, musamman kan yadda jami’an tsaro suka murƙushe zanga-zangar da ta fara a Deraa a shekarar 2011.

A shekarar 2011, an kama wasu matasa a Deraa bayan da suka rubuta kalaman adawa da gwamnati a jikin bangon wata makaranta. An azabtar da wasu daga cikinsu, lamarin da ya haifar da zanga-zangar adawa da gwamnatin Assad.

Martanin da jami’an tsaro suka mayar wa masu zanga-zangar ya ƙara rura wutar rikicin, wanda daga bisani ya rikiɗe zuwa yaƙin basasa da ya ɗauki kusan shekaru 14.

ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama sun tattara bayanan kashe-kashe da azabtarwa da jami’an tsaron gwamnatin Assad suka aikata a Deraa a farkon rikicin.

Human Rights Watch ta ce sama da mutane 30 aka kashe a harin da aka kai kan Masallacin al-Omari a watan Maris na 2011, yayin da wasu hare-hare a watan Afrilu na wannan shekarar suka sake hallaka masu zanga-zanga da dama.

A yayin yaƙin, Syria ta fuskanci munanan laifuka da suka haɗa da kisa, azabtarwa da kuma hare-haren da suka shafi fararen hula. Rikicin ya yi sanadin mutuwar kusan mutane 500,000.

Bashar al-Assad ya karɓi shugabancin Syria a shekarar 2000 bayan rasuwar mahaifinsa, Hafez al-Assad, wanda ya mulki ƙasar tsawon kusan shekaru 30.

Amma mulkinsa ya fuskanci babban ƙalubale a shekarar 2011, lokacin da zanga-zangar neman sauyin siyasa ta bazu a faɗin ƙasar.

Yaƙin ya ci gaba na tsawon shekaru, inda gwamnatin Assad ta dogara sosai kan taimakon Rasha da Iran wajen riƙe madafun iko.

A ƙarshen shekarar 2024 ne dakarun ‘yan tawaye ƙarƙashin jagorancin Hayat Tahrir al-Sham suka kai farmaki kan manyan biranen ƙasar tare da kwace Damascus.

Hakan ya kawo ƙarshen mulkin Assad na tsawon shekaru 24, tare da kawo ƙarshen kusan rabin karni na mulkin dangin Assad a Syria.

Bashar Assad da ɗan uwansa Maher sun tsere zuwa Rasha bayan faɗuwar gwamnatin, inda aka ba su mafaka.

By ukarofi

Leave a Reply