Daga JOHN D. WADA a Lafia
Daraktan kasafi a ma’aikatar kuɗi da kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki ta jihar Nasarawa Akolo Peters Ataka ya musanta zargin cewa gwamnatin jihar ta yi watsi da mazaɓar Sanatan Kudancin jihar musamman ƙananan hukumomin Obi da Doma da Awe da kuma Keana a cikin kasafin kuɗin shekarar 2026.
Peters Ataka wanda ya bayyana kasafin a matsayin “kasafin haɗin kai na dabaru”, yana mai cewa an tsara shi ne domin ya shafi kowane fanni a jihar kuma ya tabbatar da cewa mazaɓu uku na sanata da ake dasu a jihar duk sun amfana da shirye-shirye da ayyukan gwamnati ta kasafin.
Ya bayyana haka ne ga manema labarai a Lafia, babban birnin jihar yana mai jaddada cewa ayyukan gwamnati ana gudanar da su ne a matakai-matakai kuma ana iya aiwatar dasu ne a wurare da lokuta daban-daban. Wannan ne yasa da wahala a iya auna yadda aka raba kasafin kawai bisa ababen more rayuwa da ake gani.
Ya kuma bayyana cewa wasu ayyukan gwamnati ba ginannun abubuwa ba ne sai ayyuka kamar samar da kayan noma da horarwa da tsaro da sauran su.
Akolo Ataka Peters ya kuma ce mazaɓar Kudancin jihar ta amfana matuƙa da irin waɗannan ayyuka musamman ta hanyar ƙoƙarin gwamnati na inganta tsaro domin mazauna yankin su gudanar da ayyukansu cikin lumana.
Ya ce birnin Lafiya wanda shine babban birnin jihar dake Kudancin jihar ta amfana da manyan ayyukan more rayuwar ciki har da gina sabuwar sakatariyar gwamnati da samar da taraktoci da kayan noma ga manoman da suka amfana da dai sauran su.
A cewarsa daga cikin ayyukan da ake cigaba da yi a yankin akwai ayyuka a Doma da kuma gyaran babban asibitin Tunga dake ƙaramar hukumar Awe.
Ya ce gwamnati na kuma aiwatar da ayyukan ne a hankali saboda shekaru huɗu na mulki ba su da yawa ba yana mai cewa ana shirin tsara tsarin dabarun shekaru 10 domin daukar ayyukan da za a yi tsawon shekaru da dama.
Daraktan kasafin ya musanta cewa an bar ƙananan hukumomin na Obi da Doma da Awe da Keana a kasafin na 2026 inda ya ƙara cewa gwamnati ta ƙuduri aniyar tabbatar da cewa kowane yanki ya samu sakamako mai amfani da ma’ana.
