Yari ya bada tallafin N12.5M ga zawiyyah 43 a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Abdulaziz Yari Abubakar, mai wakiltar mazaɓar Zamfara ta Yamma, ya bayar da gudunmuwar shanu 43, buhunan shinkafa 356 da Naira miliyan 12,500,000 ga zawiyyah guda 43 da ke faɗin ƙananan hukumomin jihar Zamfara 14 domin gudanar da bikin Mauludi.

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Hon. Ibrahim Muhammad, shugaban kwamitin yaɗa labarai, Sanata Yari ya buƙaci al’ummar Musulmi da su yi amfani da wannan damar wajen yi wa Nijeriya addu’ar zaman lafiya, haɗin kai da ci gaban ƙasa, tare da roƙon Allah ya ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa jagora.

An kaddamar da rabon kayayyakin ne a Masallacin Juma’a na Marigayi Muhammadu Buhari da ke Unguwar Gwaza, wanda Hon. Sani Garba Gusau ya jagoranta.

Garba ya bayyana hakan a matsayin wani ɓangare na tallafin da Sanata Yari ke bai wa ƙungiyoyin addinin musulunci a duk shekara domin samun damar gudanar da Mauludi cikin kwanciyar hankali.

A yayin taron, Liman Isah Unguwar Gwaza ya yi addu’o’i na musamman ga Sanata Yari da Shugaba Tinubu kafin babban zaɓen 2027, da kuma ci gaba da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Najeriya.

Sanata Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, ya jaddada ƙudirinsa na kare lafiyar ‘yan ƙasa da kuma tallafa wa cibiyoyin addini a faɗin jihar.

By ukarofi

Leave a Reply