Tinubu zai yi jawabi a taron Majalisar Ɗinkin Duniya ranar 23 ga Satumba

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaba Bola Tinubu zai haɗu da jagororin ƙasashen duniya a taron Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD) karo na 81 (UNGA 81), inda aka tsara zai gabatar da jawabi a New York, a ranar Laraba, 23 ga Satumba, 2026.

Manhaja ta ruwaito cewa, an zaɓi Tinubu ne matsayin mai jawabi na 10 yayin zangon safe a rana ta biyu ta babban taron tafka muhawara (high-level General Debate), wanda za a gudanar a tsakanin ranakun 22 da 28 ga Satumba a hedikwatar Amurkan.

A yadda aka tsara, Shugaban Nijeriyar zai yi jawabin nasa ne yayin zangon safe, inda ake sa ran ya fara daga ƙarfe 11:30 zuwa lokacin rana a New York, wato kwatankwacin ƙarfe 4:30 na yamma a lokacin Nijeriya.

Tinubu zai shiga sahun jagororin duniya guda 193 a babban taron ciki har da sama da shugabannin ƙasashe da gwamnatoci 150, da kuma sama da mataimakan shugabannin ƙasashe 40, mataimaka firaminista, ministoci da wasu manyan jami’an gwamnati.

Shugaba Luiz da Silva na Brazil shi ne wanda zai buɗe taron da jawabinsa a ranar 22 ga Satumba, inda bayan haka ne Shugaba Donald Trump mai masaukin baƙi zai bi masa, sannan sauran jagorori su yi nasu daga bisani.

Khalilur Rahman na ƙasar Bangladesh ne zai jagoranci UNGA na 81 mai taken: ” Restoring trust, managing transformation: A United Nation that delivers for all”, wato Dawo da yarda, gudanar da sauyi: Haɗakar ƙasashe da ke warwara ga baki ɗaya.

Haka kuma, Shugaba Tinubu zai gana da Sakatare-Janar mai barin gado, António Guterres, wanda wa’adinsa biyu zai ƙare a ranar 31 ga Disamba 2026.

By Babaji

Leave a Reply