
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
‘Yan bindiga sun yi awon-gaba da mutane a wasu ƙauyuka da ke Ƙaramar Hukumar Borgo ta Jihar Neja, ciki har da waɗanda suke kan hanyar koma wa gidajensu bayan kammala sallar Juma’a.
Al’amarin ya auku ne a ranar Juma’a a jim-kaɗan bayan kammala Sallar Juma’a a babban masallacin ƙauyen Dekara, inda wasu ‘yan bindiga suka far wa jama’a tare da yin awon-gaba da masu ibada daga ƙauyukan Gidan Zana, Masaka da Sabon Gida. Daga cikin waɗanda aka sace akwai wani dattijo mai shekara 90 wanda mahaifi ne ga Dagacin Dekara, lamarin da ya jefe al’umma cikin firgici.
Majiyoyin tsaro da shaidu sun tabbatar da cewa maharan sun ƙaddamar da garkuwar ne a ƙauyukan da al’amarin ya shafa, saidai ba a iya tantance adadin waɗanda aka sace ba.
Kakakin Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja, Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar al’amarin kuma ya ce hukumomin tsaro sun tura jami’ai domin gudanar da atisayen ceto. Sannan, ya ce babu wani rahoton mutuwa da aka tabbatar a sanadiyyar harin, kuma ana gudanar da aikin gano gurin da aka kai mutanen da ƙoƙarin kamo masu hannu a ciki.
Abiodun ya ƙara da cewa, akwai wata gada da ke kai mutane zuwa yankunan ƙauyukan wadda ta lalace, wanda a saboda haka ayyukan dakarun tsaro ke fuskantar tsaikon jinkiri wajen ƙaddamar da atisaye.
