
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Shugaban rundunar sojin Uganda, Muhoozi Kainerugaba, wanda shi ne ɗan Shugaba mafi daɗewa kan karagar mulkin ƙasar, Yoweri Museveni, ya bayyana aniyarsa ta fitowa takara a zaɓen 2031 na ƙasar, lamarin da ke nuna yana son zama magajin mahaifin nasa a muƙamin.
Kainerugaba mai shekaru 52 ya yi wannan iƙirari ne a wasu wallafe-wallafe da aka yi a kafar X, ranar Talata. Hakan na zuwa ne bayan sama da shekaru 40 da mahaifinsa ke jagorantar ragamar siyasar ƙasar.
“Zan nemi takarar babban ofishin ƙasar a 2031. Kuma za mu yi nasara da yardar Ubangiji Maɗaukaki,” inji Kainerugaba.
Ya kuma yi iƙirarin cewa goyon bayan mahaifinsa zai taimaka masa wajen lashe zaɓen cikin sauƙi, yana mai fatan samun kaso 90 na ƙuri’un zaɓen a 2031.
Tun tsawon shekaru da dama ana ganin Kainerugaba a matsayin wanda zai gaji mahaifin nasa a muƙamin shugaban ƙasar, wanda ke jagorantar Uganda tun a 1986, batun da ya janyo hankalin al’umma.
Hakan ya biyo bayan matakin ɗan ne na sake mara wa mahaifin nasa baya a zaɓen Junairun 2027 da ke cigaba da kusantowa.
