TCN ya yi wa AEDC martani kan dalilan rashin samun wadataccen lantarki a Abuja

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Babban Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Ƙasa TCN, ya bayyana kalaman Kamfanin Raba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) a matsayin kuskure kuma abin ruɗarwa, inda AEDC ya danganta rage matakin raba wuta da zargin rage ƙarfin layukan lantarki daga tashar wuta ta Shiroro.

A wata takarda da ya fitar a ranar Laraba, TCN ya ce rage adadin lantarkin ga AEDC ya faru ne sakamakon ƙarancinsa daga rumbun lantarki na ƙasa, ba wai daga layukan tashar Shiroro ba kamar yadda AEDC ta yi iƙirari.

Da fari dai AEDC ya fitar da wata sanarwa, inda a ciki ya yi iƙirarin cewa an samu tsaiko daga wajen raba lantarki wanda ya sa Abuja da wasu sassa ba sa samun wuta yadda aka saba.

Kamfanin ya ce, adadin wutan da yake samu daga tashar Shiroro ya ragu daga megawatts 641 zuwa 314 tun a ranar 25 ga Agusta, 2026.

Saidai a martanin haka, TCN ya ce baki ɗaya layukan samarwa 330kV da ke ƙarƙashin Abuja suna da wuta, kuma babu wani tsaiko daga gare su kamar yadda AEDC ya yi iƙirari, yana mai cewa ana samun ƙarancin ne a wasu wuraren sakamakon nauyi da ya yi wa reshen yawa.

TCN ya kuma jaddada aniyarsa na cigaba da raba wadataccen wuta ga sassan Nijeriya da kuma kare ɗorewa da martabar rumbun lantarki na ƙasa.

By Babaji

Leave a Reply