Da Ɗumi-Ɗumi: Shugaban NPC, Aminu Wushishi ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Wushishi ya rasu.

Marigayin ya rasu ne a yau Juma’a, 28 ga Agusta, 2026 yayin da aka isar da labarin mutuwarsa a Minna bayan sallar Juma’a.

Shugaban na NPC wanda kuma tsohon sakataren jam’iyyar PDP ne na Jihar Neja, ya rasu ne bayan wani garen rashin lafiya.

Tsohon shugaban PDP na jihar, Barista Tanko Benji ne ya tabbatar da rasuwarsa marigayin ga jaridar Blueprint.

“Aminu ya rasu, ina cikin fushi kuma bana cikin yanayi mai kyau yanzu,” inji Benji.

By Babaji

Leave a Reply