Binance ya hana amfani da A7 Nigeria da A7 Africa bayan tsaurara matakan Kirifto

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kamfanin musayar kuɗaɗen dijital na Binance ya sanar da wani sabon mataki na tsaurara bin ƙa’idojin hada-hadar kadarorin crypto, inda ya dakatar da mu’amalar kuɗi da wasu dandamali 16, ciki har da A7 Nigeria da A7 Africa, waɗanda ke da alaƙa da masu amfani a Nijeriya.

Sabon matakin zai fara aiki ne daga 23 ga Agusta, 2026, yayin da Binance ke ci gaba da aiwatar da takunkumin a matakai daban-daban.

Binance ta ce matakin ya shafi wasu masu samar da hidimomin kadarorin crypto, kuma ta shawarci masu amfani da kada su aika ko karɓar kuɗi kai tsaye ko ta wata hanya daga dandamalan da aka sanya wa takunkumi ta hanyar Binance bayan ranar da aka ƙayyade musu.

Kamfanin ya bayyana cewa dole ne ya bi ƙa’idojin hukumomin da ke kula da harkokin kuɗi a ƙasashen da yake gudanar da ayyukansa.

“Binance na da alhakin bin ƙa’idojin da suka shafi harkokinta a yankunan da take aiki,” inji kamfanin, yana mai cewa matakan na da nufin kare dandalinsa da kadarorin masu amfani.

Ga masu amfani da cryptocurrency a Nijeriya, matakin ya fi jan hankali saboda A7 Nigeria da A7 Africa sun riga sun shiga jerin dandamalan da Binance ta fara takaita mu’amalarsu tun daga 13 ga Agusta.

Kafin hakan, Binance ta sanya wa Shelbit da Aban Tether Eɗchange takunkumi daga ranar 7 ga Agusta.

A sanarwar da ta fitar ranar 14 ga Agusta, Binance ta ce wasu karin dandamali 11 za su shiga jerin wadanda za a takaita mu’amalarsu daga 23 ga Agusta. Hakan ya kawo adadin dandamalan da matakin ya shafa zuwa 16.

Dandamalan 11 da sabon matakin zai shafa su ne Rapira, Aifory Pro, ABCeɗ, WhiteBird, NoOnecrypto, Tradeɗ, Monease, BitPapa, Eɗnode/Eɗnode Pay, HTɗ (Huobi Global SA) da EɗMO Ltd.

Sun shiga jerin dandamalan biyar da aka riga aka fara takaita hada-hadarsu, wato Shelbit da Aban Tether Eɗchange daga 7 ga Agusta, da A7 Nigeria, A7 Africa da PilotFinance daga 13 ga Agusta.

Binance ta jaddada cewa wannan mataki ba yana nufin ta cire Bitcoin, USDT ko wasu nau’ikan cryptocurrency daga dandalinta ba.

Abin da aka takaita shi ne mu’amalar da ta shafi wasu takamaiman dandamalan da aka lissafa.

Saboda haka, masu amfani da Binance za su iya ci gaba da cinikayyar kadarorin dijital kamar Bitcoin da USDT, amma aika kuɗi zuwa ko karɓa daga dandamalan da aka sanya wa takunkumi na iya fuskantar tsaiko ko dakatarwa bayan ranar da aka ƙayyade.

Binance ta kuma yi gargaɗin cewa duk wata mu’amala da aka yi da wani dandamali da aka sanya wa takunkumi bayan ranar fara aiki na iya shiga binciken bin ƙa’idoji, yayin da wallet ɗin da abin ya shafa zai iya fuskantar takunkumi na ɗan lokaci.

Kamfanin bai bayyana tsawon lokacin da irin wannan bincike zai ɗauka ba. Hakan na nufin wasu masu amfani na iya fuskantar jinkiri wajen kammala hada-hadar kuɗinsu, maimakon a ƙi mu’amalar kai tsaye a kowane hali.

By ukarofi

Leave a Reply