’Yan Nijeriya sun zama ja-gaban duba shafukan intanet na batsa, caca da AI a Yulin 2026

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan Nijeriya sun kai miliyoyin ziyara ga shafukan intanet da suka shafi abubuwan batsa, wasannin caca da kuma manhajojin ƙirƙirarriyar basira ta AI a watan Yulin 2026, kamar yadda bayanan Semrush Traffic Analytics suka nuna.

Bayanan da kamfanin Semrush ya fitar kan shafukan intanet da aka fi ziyarta a Nijeriya a watan Yuli sun nuna cewa Google ne ya kasance kan gaba, inda ya samu ziyara miliyan 318.45. A matsayi na biyu kuwa akwai YouTube, wanda ya samu ziyara miliyan 46.42.

Shafin Sɓideos, wanda ke ƙunshe da abubuwan batsa, ya zo na uku da ziyara miliyan 37.64, yayin da shafin yin caca na wasanni, SportyBet, ya kasance na huɗu da ziyara miliyan 36.28. ChatGPT, mahajar ƙirƙirarriyar basira ta AI, ta zo ta biyar a jerin, inda ta samu ziyara miliyan 35.32 a watan.

Wannan ya nuna cewa yawan zirga-zirgar ChatGPT daga Nijeriya ya ƙaru da kashi 9.81 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Yunin 2026, sannan ya karu da kashi 33.43 cikin 100 idan aka kwatanta da Yulin 2025.

Facebook ya kasance na shida da ziyara miliyan 32.85, yayin da WhatsApp ya zo na bakwai da miliyan 18.32. Shafin LibeScore, wanda ake amfani da shi wajen bibiyar sakamakon wasanni, ya kasance na takwas da ziyara miliyan 15.46.

Sai kuma wani shafin abubuwan batsa, SNSS, wanda ya samu ziyara miliyan 15.42, ya zo na tara. ɗ, wanda aka fi sani da Twitter a baya, ya kasance na 10 da ziyara miliyan 15.17. Instagram ya zo na 11 da ziyara miliyan 14.32, yayin da TikTok ya kasance na 12 da ziyara miliyan 13.38.

Shafin yin caca na wasanni, Bet9ja, ya zo na 13 da ziyara miliyan 11.61, yayin da Thenkiri ya kasance na 14 da miliyan 10.86. Wani shafin AI, Claude, ya zo na 15 da ziyara miliyan 10.23.

Semrush ta ce Claude ya samu ƙarin zirga-zirga daga Nijeriya da kashi 11.4 cikin 100 cikin wata guda, yayin da idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, zirga-zirgar shafin ta ƙaru da gagarumin kaso na 440.86 cikin 100.

Shafin Pornhub ya zo na 16 da ziyara miliyan 9.41, yayin da Stake ya samu miliyan 8.87, ya zo na 17. 1sBet ya kasance na 18 da ziyara miliyan 8.68, yayin da BetKing ya zo na 19 da miliyan 8.06.

A cewar Semrush, jadawalin ya dogara ne kan bayanan da Traffic Analytics ke tattarawa, kuma ana sabunta shi duk wata domin bibiyar sauye-sauyen da ake samu wajen amfani da shafukan intanet da kuma irin abubuwan da mutane ke nema.

Kamfanin ya ce zirga-zirgar Google ta ragu da kashi 6.58 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata, sannan ta ragu da kashi 11.13 cikin 100 idan aka kwatanta da Yulin shekarar 2025.

YouTube ma ya samu raguwar zirga-zirga da kashi 4.17 cikin 100 a wata guda, yayin da ya samu raguwar kashi 6.25 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Facebook ya samu raguwar zirga-zirga da kashi 38.92 cikin 100 cikin shekara guda, yayin da ɗ ya ragu da kashi 23.16 cikin 100 a wannan lokaci. Sai dai TikTok ya tafi akasin haka, inda zirga-zirgarsa daga Nijeriya ta ƙaru da kashi 16.49 cikin 100 cikin shekara guda.

Haka kuma, WhatsApp ya samu ƙarin zirga-zirga da kashi 16.85 cikin 100 idan aka kwatanta da watan da ya gabata, duk da cewa idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, zirga-zirgarsa ta ragu da kashi 3.55 cikin 100.

Semrush ta ce daga cikin shafuka 100 da aka fi ziyarta a Nijeriya, 87 sun fi samun masu amfani ne ta hanyar shiga shafin kai tsaye, ma’ana masu amfani sun rubuta adireshin shafin ko suka shiga ta wata hanya kai tsaye ba tare da amfani da injin bincike ba.

Shafi guda ne kawai ya fi dogaro da zirga-zirgar da ke zuwa ta injin bincike, yayin da shafuka 12 suka fi samun masu amfani ta kafafen sada zumunta. Kamfanin ya bayyana cewa an samo alƙaluman ne daga bayanan clickstream, wato bayanan da ke nuna yadda masu amfani ke zirga-zirga tsakanin shafukan intanet.

Semrush ta ce bayanan sun samo asali ne daga ayyukan sama da masu amfani miliyan 200 da aka ɓoye bayanansu domin kada a iya gano ainihin su waye. Ta ƙara da cewa an yi amfani da na’urorin AI wajen nazarin bayanan da aka samu daga majiyoyin da kamfanin ya mallaka da kuma wasu majiyoyin waje, domin samar da kiyasin yawan zirga-zirgar shafukan.

Sai dai Semrush ta yi gargaɗin cewa waɗannan alƙaluma ba sa nuna adadin ’yan Nijeriya na musamman da suka shiga shafukan ba. Abin da suke nuna shi ne yawan ziyara. Wannan na nufin mutum ɗaya zai iya shiga shafi guda sau da dama a cikin watan, kuma kowace ziyara na iya shiga cikin jimillar alƙaluman da aka bayar.

By ukarofi

Leave a Reply