Gwamna Lawal ya jagoranci babban taron shugabannin kamfanoni na 2026 kan zuba jari a Zamfara

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya jagoranci Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 (CEO Forum), inda aka maida hankali kan yadda za a haɗa jari da damar kasuwanci tare da daidaita manufofin kasuwanci domin bunƙasa zuba jari da ci gaban tattalin arziki mai amfani ga kowa a Jihar Zamfara.

A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar a ranar Talata, ya ce gwamnan ya gabatar da hawabin musamman kan manufofin gwamnati yayin taron wanda Global Compact Network Nigeria ya shirya.

An gudanar da taron na bana a Legas, ƙarƙashin taken: “Samar da Kuɗaɗen Gina Makoma Mai Daraja: Daidaita Ayyukan Kasuwanci, Manufofi da Jari.”

Taron ya kasance wani zama na musamman da ya haɗa manyan shugabannin kamfanoni da jami’an gwamnati, inda aka samu manyan ’yan kasuwa daga fannoni daban-daban, ciki har da man fetur da iskar gas, makamashi, masana’antu, gine-gine da ababen more rayuwa.

Haka kuma, taron ya samu halartar kwamishinonin kasuwanci, jami’an diflomasiyya da abokan hulɗar ci gaban ƙasa da ƙasa.

A yayin jawabin nasa, Gwamna Lawal ya yi bayani kan yadda jihohi ke fafatawa wajen jawo hankalin masu zuba jari masu zaman kansu, musamman a daidai lokacin da masu jarin ke ƙara tsaurara matakan zaɓen wuraren da za su saka kuɗaɗensu.

Ya kuma yi bayani kan abin da ke bambanta wata dama ta tattalin arziki da kuma damar da ta dace da a zuba jari a cikinta.

Gwamnan ya bayyana yadda gwamnatin Zamfara ƙarƙashin jagorancinsa ke ƙoƙarin cike wannan gibi, ta yadda za a ƙarfafa amincewar masu zuba jari tare da samar da sakamakon tattalin arziki mai ma’ana ga al’ummar jihar.

An shirya taron ne domin samar da wata kafa da za ta haɗa shugabannin kasuwanci, jami’an gwamnati da masu zuba jari, domin su daidaita matakan da suke ɗauka tare da buɗe ƙofofin zuba jari mai amfani da kuma bunƙasa tattalin arziki da zai shafi kowane ɓangare na al’umma.

Taron na bana ya mayar da hankali kan yadda za a haɗa jari da damar zuba jari, ta hanyar gano kasuwanci, fannoni da ayyukan raya ƙasa masu alƙawari waɗanda ke fuskantar matsalar samun kuɗaɗen gudanarwa, da kuma hanyoyin da za a bi wajen jawo masu zuba jari.

A wani ɓangare kuma, taron ya tattauna batun “Ribar Darajar Rayuwa” (Dignity Dividend), wato yadda zuba jari da bunƙasar tattalin arziki za su iya haifar da ingantattun guraben ayyukan yi, ƙarfafa kamfanoni, ƙara yawan aiki, samar da ƙarin darajar kayayyaki a cikin gida da kuma faɗaɗa damar jama’a na shiga harkokin tattalin arziki.

Taron ya kuma mayar da hankali kan samar da ƙwaƙƙwaran alƙawura da za a iya aiwatarwa, inda aka tsara takamaiman matakai da haɗin gwiwa da cibiyoyin da suka halarci taron za su iya aiwatarwa cikin watanni 6 zuwa 12 masu zuwa.

Daga cikin fitattun masu jawabi a taron akwai shugabannin zartarwa na First Bank Group, Access Bank, Flour Mills of Nigeria Plc, Nigeria Economic Summit Group, Nigerian Exchange Group, Chellarams Plc, SecureID Group da Greenwich Merchant Bank Plc, da sauran manyan ’yan kasuwa.

Masu shirya taron sun ce za a kammala zaman ne da gabatar da Business Value and Sustainability Platform (BVSP) kai tsaye, wadda wata ƙungiyar haɗin gwiwa ce ta dindindin da ba ta da tsauraran matakai, wadda ta ƙunshi masu ruwa da tsaki daga ɓangarorin kasuwanci, jari da manufofin gwamnati.

Sun ce manufar dandalin ita ce ci gaba da tattaunawar da aka fara, ciki har da taimakawa wajen tsara irin gudunmawar da kamfanoni masu zaman kansu za su bayar a ayyukan Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya (UNGA) na mako mai matuƙar muhimmanci, wato High-Level Week.

By Babaji

Leave a Reply