
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbatar da tantance makarantun kuɗi guda 123 bayan cika sharuɗɗa da ƙa’idojin karantarwa da koyo ga yara da suka cika a jihar.
Gwamnatin ta kuma gano wasu makarantu 508 na masu zaman kansu guda 242 da aka tantance domin tabbatar suna kiyaye ƙa’idojin koyon karatu da karantarwa.
Shugabar kwamitin tabbatar da biyayya ga tsarin gudanarwar makarantun kuɗi a jihar, Kulu Na’ala ce ta bayyana haka yayin gabatar da rahoton kwamitin a Gusau, ranar Talata. Ta ce, daga cikin alhakin da ke kan kwamitin, akwai tabbatar da cewa ire-iren makarantun sun cika sharuɗɗan aminci, doka da ƙarfin gudanarwa bisa tsarin gwamnatin jihar kan ilimi.
Ta bayyana cewa, an yi nazari akan guda 242 daga cikin 508 da aka gano; 123 suna kan tsari yayin da 119 kuma suna kan matsakaici ko kuma ƙarancin tsarin gudanarwa.
A cewarta, kwamitin ya cimma wasu nasarori yayin atisayen, waɗanda suka haɗa da gano bashin Naira miliyan 23 da kuma biyan su ga hukumar tattara haraji ta jihar. Haka kuma, ta ce an horar da masu makarantun kan yadda za su biya harajinsu a zamanance ta yadda za su guje wa tara bashin haraji mai yawa a wuyansu.
Kazalika, ta jaddada aniyar kwamitin ta cigaba da ƙarfafa sauke nauyin haraji a fannin ilimi, tana mai kira ga majalisar dokokin jihar da ta ba su goyon baya wajen tabbatar da biyayya ga tsare-tsaren, sauƙaƙe hanyoyin amincewa da sanya ido ga harkokin gudanar da makarantu masu zaman kansu a faɗin jihar.
