Wani sabon salon dabarun yaƙi da matsalar tsaro a Nijeriya

Spread the love

Matsalolin tsaron da suka daɗe suna addabar Nijeriya sun sake tabbatar da wani muhimmin abu: jarumtar dakarunmu a fagen daga, amma duk da muhimmancinta, ita kaɗai ba za ta iya tabbatar da ɗorewar tsaron ƙasa ba. ƙasar da ke fuskantar barazanar tsaro mai sarƙaƙiya, wadda kuma ke sauya salo lokaci zuwa lokaci, na buƙatar ba wai kawai ƙarfin tunkarar hari bayan ya auku ba, har ma da hangen nesa da zai taimaka wajen gano barazana tun kafin ta girma ta rikiɗe zuwa babbar matsalar tsaro.

A kan wannan mizani ne ya kamata a kalli kafa Kwamitin Shugaban ƙasa kan Tantance Barazanar Tsaro ta ƙasa da Tsarin Ayyukan Tsaron ƙasa na Shekaru Biyar a matsayin wani mataki da ya cancanci cikakken goyon baya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) ne ya ƙaddamar da kwamitin a ranar Larabar da ta gabata, a madadin Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, inda aka ba shi muhimmin aiki da zai kammala cikin kwanaki 90. Aikin shi ne samar da cikakken rahoton tantance barazanar tsaron ƙasa, tare da tsara wani shirin ayyukan tsaro na shekaru biyar da za a riƙa sabuntawa, domin miƙa shi ga Shugaban ƙasa ya duba.

Nauyin da aka ɗora wa kwamitin ba ƙarami ba ne, domin ya shafi ginshiƙan tsaron aasar baki ɗaya. Daga cikin abubuwan da ake sa ran zai yi akwai gano barazanar da ake fuskanta a yanzu da kuma waɗanda ka iya kunno kai nan gaba; tantance irin gaggawar kowace barazana da tasirinta ga dabarun tsaron ƙasa; tsara abubuwan da ya kamata a ba fifiko wajen gudanar da ayyukan tsaro; gano giɓin da ke akwai a ƙarfin rundunonin tsaro; da kuma tantance yawan ma’aikata, kayan aiki, bayanan sirri, dabarun sufuri da samar da kayayyaki, fasaha da ababen more rayuwa da ake buƙata domin tinkarar waɗannan barazana.

Haka kuma, ana buƙatar kwamitin ya tsara abubuwan da ya kamata a fi bai wa fifiko wajen sayen kayan aikin tsaro, bisa la’akari da ainihin barazanar da ake fuskanta da kuma buƙatun ayyukan soji, tare da tsara lokutan aiwatar da shawarwarin cikin haƙiƙa. Ya kuma kamata ya samar da hanyoyin bibiyar ci gaban ayyukan da kuma auna sakamakon da aka samu.

Gwamnatocin Nijeriya da suka gabata sun shafe shekaru suna ƙirƙirar manufofi, tsare-tsare da dabaru daban-daban domin ƙarfafa tsaron cikin gida da na waje. Duk da haka, tare da duk waɗannan ƙoƙarce-ƙoƙarce da kuma irin sadaukarwar da jami’an soji da sauran hukumomin tsaro suka yi, matsalolin tsaro sun ci gaba da wanzuwa, a wasu wuraren ma abin ya ƙara ta’azzara.

Lamarin ya fi tayar da hankali a sassan Arewa, inda ta’addanci, ’yan fashin daji, garkuwa da mutane da sauran nau’o’in aikata muggan laifuka da ƙarfi suke ci gaba da gwada ƙarfin gwamnati. Wannan yanayi na buƙatar ƙarin ƙoƙari da kuma samar da sabbin dabarun da za su dace da irin barazanar da ake fuskanta a wannan zamani.

Gwamnatin Tinubu ta riga ta nuna aniyarta ta yin garambawul a wasu sassan tsarin tafiyar da harkokin tsaro da tsaron ƙasa, ciki har da ƙirƙirar muƙamin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Gida.

Abin takaici, wasu sun yi wa wannan mataki mummunar fahimta, suna ganin kamar ƙirƙirar sabon muƙamin na nufin rage darajar ko muhimmancin Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaron ƙasa (NSA). Babu abin da ya yi nisa da wannan fahimta kamar haka.

Tsarin da aka yi wa sabon kwamitin, inda Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaron ƙasa (NSA) ke taka muhimmiyar rawa, yayin da Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Tsaron Cikin Gida ke sauƙaƙa haɗin gwiwa tsakanin ɓangarori, tare da halartar sauran hukumomi da sassan tsaro da na tsaron ƙasa, ya nuna cewa abin da ake nema shi ne haɗa ƙarfi da daidaita aiki, ba fafatawa ko kishiyantar juna ba.

Abu mafi muhimmanci kuma abin yabawa a wannan sabon tsarin shi ne yadda aka mayar da hankali kan hango barazana tun kafin ta auku.

Dole Nijeriya ta fita daga tsarin da ke jiran laifi ya auku sannan a fara neman hanyar tunkararsa. Kyakkyawan tsarin tantance barazanar tsaron ƙasa ya kamata ya bai wa gwamnati damar gano alamomin farko da kuma sabbin barazanar da ke kunno kai tun kafin su yi ƙarfi, domin a daƙile su ko kuma a takaita illar da za su iya haifarwa.

Misali, iyakokin ƙasar da ke da sauƙin ketarewa ba bisa ƙa’ida ba, da kuma shigowa da fita daga ƙasashe makwabta ba tare da cikakken iko ba, na daga cikin manyan abubuwan da ke buƙatar kulawa. Haka nan akwai tashe-tashen hankulan addini, ƙabilanci da na ƙabilu da ke iya tasowa; barazanar da za ta iya kawo cikas ga zaman lafiyar dimokuraɗiyya ta hanyar tayar da zaune tsaye; da sauran abubuwan da ka iya girgiza haɗin kan ƙasa da kuma tauye ikon Nijeriya na mulkin kanta.

Irin waɗannan ƙalubale ba za a iya magance su da ɗaukar mataki bayan bala’i ya faru kawai ba. Suna buƙatar tsare-tsare da bayanan sirri ke jagoranta, tare da haɗa kan hukumomi da dukkan sassan gwamnati da abin ya shafa.

Sabon tsarin da aka ƙaddamar ya ba Nijeriya wata dama ta gina irin wannan tsari—wanda zai haɗa barazana da manufofin tsaro, ƙarfin da ake da shi, albarkatun da ake buƙata da kuma sakamakon da za a iya aunawa.

Saboda haka, aikin da ke gaban wannan kwamiti yana da girma ƙwarai, amma kuma aiki ne da ba za a iya kauce masa ba. Kamar yadda Sakataren Gwamnatin Tarayya ya yi kira, ya kamata mambobin kwamitin su tunkari wannan nauyi cikin ƙwarewa, adalci, gaggawa da kishin ƙasa.

Nijeriya ta cancanci hakan, kuma ba abin da ya gaza haka ya kamata a samar mata ba.

Dole ne kwamitin ya ɗaukaka muradun ƙasa sama da muradun kowace hukuma ko sashe, ya yi aiki a matsayin ƙungiya guda da manufar kare babbar muradin Nijeriya.

Idan aka tsara wannan shiri cikin hikima, aka kuma aiwatar da shi da gaskiya da jajircewa, babu shakka zai iya zama wani muhimmin sauyi na dabarun yaƙi da matsalar tsaro a Nijeriya, tare da buɗe sabon babi a dogon ƙoƙarin ƙasar na neman zaman lafiya da ɗorewar tsaro.

By ukarofi