Arewa ce za ta fi amfana da sauye-sauyenmu — Tinubu

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ce Arewacin Nijeriya ne zai fi amfana da sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatinsa ta kawo, musamman ta fuskar manyan ayyukan more rayuwa da bunƙasa damar kasuwanci da ƙasashen maƙwabta.

Tinubu ya ce cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnati damar karkatar da kuɗaɗen da ake kashewa wajen tallafin zuwa wasu muhimman fannoni na ci gaban ƙasa.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, a wani taron tattaunawa kan manufofin gwamnati da APC Professionals Forum ta shirya a Abuja.

Gwamnatin ta ce wasu daga cikin ayyukan da Arewa za ta amfana da su sun haɗa da aikin bututun iskar gas na Ajaokuta–Kaduna–Kano (AKK), da hanyoyin Akwanga–Maiduguri da Jos–Jalingo, baya ga shirye-shiryen inganta ilimi da horar da matasa.

Tinubu ya ce inganta hanyoyin sufuri da sauran manyan ababen more rayuwa za su ƙara buɗe wa Arewa damar kasuwanci da ƙasashe maƙwabta, ciki har da Nijar, Chadi, Burkina Faso, Kamaru da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

A cewar shugaban, wannan zai taimaka wajen mayar da yankin Arewa wata babbar cibiyar kasuwanci da tattalin arziki, musamman saboda kusancinsa da ƙasashe da dama na Afirka.

Sai dai wasu ƙungiyoyin Arewa sun musanta iƙirarin cewa Arewa ce za ta fi amfana da sauye-sauyen gwamnatin.

Mai magana da yawun ƙungiyar Tuntuɓa ta Arewa (ACF), Farfesa Tukur Muhammad Baba, ya ce kalaman Tinubu abin mamaki ne, saboda shugaban bai gabatar da cikakkun bayanai da za su nuna ta wace hanya Arewa za ta fi cin gajiyar sauye-sauyen.

ACF ta ce halin da ake ciki na talauci, rashin tsaro, koma bayan noma da ƙarancin ababen more rayuwa a yankin Arewa ya nuna akasin abin da shugaban ya bayyana.

Shi ma Shugaban ƙungiyar Haɗin Kan Mutanen Arewa ta Tsakiya ta ƙasa, Dokta Bitrus Pogu, ya ce manufofi irin su cire tallafin man fetur da ƙaddamar da amfani da iskar gas mai matsewa (CNG) manufofi ne na ƙasa baki ɗaya.

Ya ce saboda haka ba za a ce wani yanki ne kaɗai zai fi cin gajiyarsu ba, domin ana aiwatar da manufofin ne domin amfanin ɗaukacin ’yan Nijeriya.

Bayanai sun nuna cewa batun wanda zai fi cin gajiyar sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu ya haifar da mabanbantan ra’ayoyi, yayin da gwamnatin ke jaddada cewa manyan ayyukan more rayuwa da hanyoyin kasuwanci za su ƙara buɗe damar tattalin arziki ga yankin Arewa.

By ukarofi