
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnatin Tarayya ta musanta bayar da goyon baya ga yunƙurin kifar da gwamnatin soji ta Jamhuriyar Nijar, tana mai watsi da iƙirarin cewa hakan ya samu goyon bayan Ƙungiyar Ƙasashe Afirka ta Yamma masu Ƙarfin Tattalin Arziƙi (ECOWAS) kuma musamman yadda aka danganta da Nijeriya.
Ƙaramin Ministan Harkokin Waje, Ambasada Sola Enikanolaiye ne ya bayyana haka a wata takarda da ke ɗauke da sanya hannunsa a ranar Alhamis, inda ya bayyana iƙirarin, wanda ake yaɗawa a kafafen Soshiyal Mediya a matsayin ƙoƙarin ruɗar da jama’a da ɓata wa Nijeriya suna.
Enikanolaiye ya ce an ankarar da ma’aikatar bisa iƙirarin ƙarya da ke nuna cewa yunƙurin juyin mulkin Nijar na kwanan nan ya samu goyon bayan ECOWAS da amincewar Nijeriya.
A cewar ministan, Nijeriya ƙasa ce mai son zaman lafiya, bayar da kariya ga hukunce-hukuncen doka kuma jinshiƙin dimukraɗiyya da ɗorewa ba a iya Afirka ta Yamma ba, hatta a yankin Sahel da ma nahiyar Afirka baki ɗaya. Ya ce, ba yadda za a yi Nijeriya ta bai wa haramci ko sauyin gwamnati ta haramtacciya hanya goyon baya ko da kuwa hakan ya shafi kowace ƙasa.
Ya ƙara da cewa, Nijeriya tana kallon dukkan wani salo na sauya gwamnati da bai halatta ba a matsayin abin da ba za ta taɓa goya wa baya ba, yana mai cewa Nijeriya na son zaman lafiya, tsaro, dimukraɗiyya da ci-gaba ga Nijar da yankin Sahel a matsayinta na maƙociyarta da suka haɗu a ababe da dama ciki har da tarihi da al’adu.
Akan haka ne ya roƙi mahukunta da al’ummar Nijar da da ke gida da waje da su yi watsi da bidiyoyi da bayanan ƙarya da wasu ke yaɗawa da nufin tayar da zaune-tsaye.
