NFIU ta bibiyi ma’amalolin kuɗi miliyan 41.7 don daƙile ta’addanci da laifukan tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Leƙen Asirin Kuɗaɗe ta Nijeriya (NFIU) ta ƙara tsaurara matakan amfani da bayanan harkokin kuɗi wajen daƙile hanyoyin samar da kuɗaɗen ta’addanci, safarar kuɗaɗen haram, zagon ƙasa ga tattalin arzikin ƙasa da kuma tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata manyan laifuka a faɗin ƙasar.

Shugabar Sashen Sadarwa da Dabarun Yaɗa Bayanai na hukumar, Aishatu Bantam, ce ta bayyana hakan a ranar Talata a Abuja, yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwar hukumomin tsaro da Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro ya shirya.

Bantam ta ce, hukumar na ƙara zurfafa binciken hanyoyin da kuɗaɗen masu aikata laifuka ke bi, domin gano alaƙar kuɗi da ke tsakanin ’yan ta’adda, masu garkuwa da mutane, masu safarar miyagun ƙwayoyi, ’yan damfara ta yanar gizo da sauran ƙungiyoyin masu aikata laifuka.

Ta ce, manufar wannan sabon salo ita ce ƙarfafa ayyukan tsaro na yau da kullum ta hanyar gano waɗanda ke ɗaukar nauyin laifukan, masu taimaka musu, waɗanda ke amfana da kuɗaɗen haram da kuma dukiyoyin da aka samu ta hanyar aikata laifuka.

A cewarta, bin diddigin harkokin kuɗi na da matuƙar muhimmanci wajen tarwatsa ƙungiyoyin masu aikata laifuka, domin a ƙarshe dai babu wata babbar hanyar aikata laifi da za ta iya ɗorewa ba tare da samun kuɗaɗen shiga da hanyoyin karkatar da su ba.

Bantam ta ce NFIU ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro da tabbatar da doka, domin gudanar da bincike na musamman kan manyan shari’o’in da suka shafi samar da kuɗaɗen ta’addanci da kuma zirga-zirgar kuɗaɗen haram.

Ta ƙara da cewa, hukumar ta kuma zurfafa hulɗa da hukumomin sa ido da na tabbatar da doka, domin gano ma’amalolin kuɗi da ake zargi da rashin gaskiya tare da gano giɓin da masu laifi za su iya amfani da shi a tsarin hada-hadar kuɗin Nijeriya.

Ta ce, bayanan da NFIU ta tattara da nazari a shekarar 2025 sun nuna irin ɗimbin bayanan kuɗi da ke hannun masu bincike, inda hukumomi da cibiyoyin da doka ta wajabta musu bayar da rahoto suka gabatar da rahotannin hada-hadar kuɗi sama da miliyan 41.7.

Baya ga haka, ta ce an gabatar da rahotannin ma’amalolin kuɗi 42,082 da ake zargi da kasancewa na tuhuma, da kuma rahotannin wasu ayyukan kuɗi 10,513 da ake ganin suna da alamun da suka dace da bincike.

A cewar Bantam, laifukan da suka shafi haraji da damfara ne suka fi yawa, inda suka kai kashi 51 cikin 100 na bayanan leƙen asirin kuɗi da aka rarraba a cikin manyan nau’o’in laifuka 10 da hukumar ke sa ido a kansu.

Ta ce binciken hukumar ya kuma gano wasu sabbin dabarun da ake amfani da su wajen samar da kuɗaɗen ta’addanci, ciki har da amfani da asusun wasu mutane a matsayin wakilai, asusun da ake amfani da su wajen karɓa da tura kuɗaɗe ba tare da masu asusun sun san ainihin manufar ba, katunan SIM da aka riga aka yi musu rajista, tara kuɗi ta kafafen sada zumunta, da kuma rarraba kuɗaɗen tura wa mutane zuwa ƙananan ma’amaloli domin ɓoye asalinsu.

Ta ce waɗannan abubuwa sun ƙara nuna muhimmancin tsaurara matakan tantance abokan hulɗa da cibiyoyin kuɗi, binciken bayanan abokan hulɗa da kuma sanya ido kan harkokin kuɗi bisa bayanan sirri da aka tattara.

Shugabar Sadarwar ta NFIU ta ce ƙwarewar Nijeriya wajen amfani da bayanan kuɗi wajen yaƙi da laifuka ta samu karɓuwa a duniya, bayan NFIU da Hukumar Yaƙi da Masu Yi Wa Tattalin Arzikin ƙasa Ta’annati (EFCC) sun lashe lambar yabo ta UNODC-World Bank-Egmont Group Stolen Asset Recoɓery Initiatiɓe Award. Ta ce an ba hukumomin biyu lambar yabon ne saboda nasarar da suka samu wajen haɗa ƙarfi wajen bin diddigin dukiyoyin da aka samu ta haramtacciyar hanya da kuma ƙwato su.

Bantam ta kuma ce NFIU ta ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa da Hukumar Yaƙi da Manyan Laifuka ta Birtaniya (NCA), Amurka da sauran abokan hulɗar ƙasa da ƙasa. A cewarta, haɗin gwiwar ya fi karkata ne kan musayar bayanan sirri, yaƙi da samar da kuɗaɗen ta’addanci, manyan laifukan kuɗi da suka ratsa iyakokin ƙasashe, gano sabbin dabarun aikata laifuka da kuma ƙarfafa ƙwarewar jami’an bincike.

Ta ce NFIU na kuma aiki tare da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya wajen inganta tsarin tura shari’o’in da ke buƙatar zurfafa binciken kuɗi, musamman waɗanda suka shafi ta’addanci, ’yan fashin daji da satar ɗanyen mai.

Bantam ta ce halartar NFIU wajen tantance sabon ƙididdigar Haɗarin Wanke Kuɗaɗen Haram da Samar da Kuɗaɗan Ta’addanci ta ƙasa ya ƙara wa Nijeriya damar gano sabbin barazanar da ke kunno kai da kuma ɗaukar matakan dakile su tun kafin su ƙara yaɗuwa.

Ta tabbatar da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin cikin gida da abokan hulɗar ƙasa da ƙasa, domin hana masu aikata laifuka amfani da tsarin hada-hadar kuɗin Nijeriya wajen ɓoye ribar da suka samu ta haramtacciyar hanya. Ta ce, babban abin da hukumar ta sa a gaba shi ne: “gano kuɗin, tona asirin hanyoyin sadarwar masu laifi, daƙile hanyoyin samar da kuɗaɗen laifi, tare da taimakawa wajen kwato dukiyar da aka samu ta haramtacciyar hanya.

By ukarofi