Alanis Morissette ta kai tsohon manajan rangadinta ƙara kan zargin yi mata barazana

Spread the love

Daga AISHA ASAS 

Wata sabuwar matsala ta shiga tsakanin fitacciyar mawaƙiya Alanis Morissette da tsohon manajan rangadinta, bayan mawaƙiyar ta shigar da ƙara tana zarginsa da wani shiri na matsa mata lamba da kuma kokarin yi mata barazana.

Morissette ta kai karar Keren Urinov a wata kotun tarayya da ke Los Angeles, inda ta yi zargin cewa tsohon ma’aikacin nata ya shiga wani shiri na abin da ta kira “blackmail”, wato kokarin tsoratar da ita da wasu bayanai domin samun abin da yake so.

A cewar bayanan da ke cikin karar, rikicin ya samo asali ne daga wani lamari da ya shafi wata jaka da jami’an tsaron kan iyaka suka kama a filin jirgin sama a shekarar 2025, inda aka ce an samu wasu abubuwa da ake zargin kwayoyi ne a cikinta.

Morissette ta yi zargin cewa daga baya Urinov ya yi amfani da wannan lamari wajen matsa mata lamba, har ta kai ga abin da mawakiya ta bayyana a matsayin wata dabara da aka tsara domin tilasta mata amincewa da wasu sharuɗɗa.

A nata ɓangaren, karar ta ƙunshi zarge-zargen damfara, neman karɓar kuɗi ta hanyar barazana da kuma ba da bayanan da ba daidai ba, yayin da ake sa ran ɓangaren da ake zargi zai samu damar mayar da martani ga zarge-zargen.

Sabon rikicin ya jawo hankali saboda Morissette ta shafe shekaru tana cikin manyan sunayen masana’antar waƙoƙin duniya, kuma batun ya sake nuna yadda saɓanin da ya taso tsakanin fitattun mawaka da mutanen da ke aiki tare da su kan iya rikiɗewa zuwa shari’a.

By ukarofi

Leave a Reply