
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Jigawa, Malam (Dr.) Umar A. Namadi, FCA, ya amince da naɗin Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani a matsayin Sarkin Masarautar Gumel na 17.
Wannan naɗi ya biyo bayan shawarwari daga majalisar masu zaɓen sarki da majalisar sarakunan jihar Jigawa.
Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani ya riƙe muƙamin Ciroman Gumel kuma Hakimin Gundumar Bosuwa. Ya kuma riƙe muƙamin daraktan Tsaron Yanar Gizo a Hukumar Ci-gaban Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA).
A wata sanarwa daga Sakataren gwamnatin jihar, Malam Bala Ibrahim ya fitar, ya ce Gwamna Namadi ya bayyana godiyarsa ga majalisar masu zaɓen sarki ta Masarautar Gumel ƙarƙashin jagorancin Wazirin Gumel, Alhaji Adamu Muhammad Nasoro da sauran mambobi bisa rawar da suka taka wajen zaɓo basaraken.
Haka kuma, ya yi godiya ga masu martaba sarakunan Haɗejia, Kazaure, Ringim da Dutse, waɗanda suka samar da majalisar sarakunan jihar bisa shawarwarinsu yayin al’amarin.
A cewar sanarwar, Gwamna Namadi a madadin gwamnatin Jigawa, ya taya Dakta Lawan Ahmed Muhammad Sani murna kan naɗa shi a matsayin Sarkin Gumel na 17. Ya yi masa fatan cimma nasarori da samun shekaru masu albarka kan karagar mulkin, yana mai fatan zamansa a muƙamin ya amfani Masarautar Gumel da Jihar Jigawa da ma ƙasa baki ɗaya.
