‘Yan bindiga sun kashe jami’in kuɗi na jami’ar NOUN a Zamfara

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Jami’ar NOUN ta ƙasa ta Najeriya, NOUN, tana cikin jimami bayan kisan Malam Nasiru Marafa Gusau, wanda wasu da ake zargi ‘yan ta’adda ne suka harbe shi yau Lahadi, yayin da yake komawa Abuja daga Gusau, Jihar Zamfara.

A cewar wata sanarwa a hukumance wacce magatakarda kuma sakataren majalisar jami’ar, Oladipo Adetayo Ajayi ya sanya wa hannu, lamarin ya faru ne a yankin Tsafe zuwa Magazu yayin da Marafa ke kan hanyarsa ta komawa Abuja daga Gusau.

“Jami’an da ke tare da shi sun sanar da hukumomin jami’ar game da harin”.

Shugaban jami’ar, a madadin majalisar gudanarwa, majalisar dattawa, ma’aikata da ɗaliban jami’ar NOUN, ta bayyana lamarin a matsayin mutuwar ba zato ba tsammani da kuma babban rashi ga al’ummar jami’ar.

Jami’ar ta ce Marafa ma’aikaci ne mai himma da jajircewa wanda ya yi wa cibiyar hidima cikin girmamawa kuma ya riƙe muƙamai daban-daban kafin naɗinsa a matsayin jami’in kuɗi a watan Satumba na 2026. Sanarwar ta ce

A cewar sanarwar ya karɓi wannan matsayi da ƙarfin hali da kuma jajircewa wajen ci gaban jami’ar.”

Jami’ar ta bayyana shi a matsayin fitaccen abokin aiki, mai himma da kuma mamba mai daraja na jami’ar ta NOUN.

Kisan ya ƙara dagula matsalolin tsaro a kan manyan hanyoyi a Zamfara da jihohin da ke maƙwabtaka da ita, inda aka sha kai hari ga matafiya a wasu lokutan.

Tuni aka binne mamacin a Gusau bisa ga tanadin addinin musulunci a yau.

By ukarofi

Leave a Reply