
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kotun zaɓen gwamnan jihar Osun ta wallafa ƙorafe-ƙorafe biyu da jam’iyyun APC da PDP suka shigar mata, waɗanda suke ƙalubalantar nasarar da Gwamna Ademola Adeleke ya sake samu.
Rahotanni sun nuna cewa kotu ta wallafa ƙorafe-ƙorafen ne a allonta na sanarwa a sakatariyarta da ke Osogbo a ranar Litinin, wanda ke nuna ɗaukar matakin shari’a kan zaɓen, wanda aka gudanar a ranar 15 ga Agusta.
An samu haka ne bayan Sakataren kotun, Pefe Belemore ya tabbatar da cewa an shigar da ƙorafe-ƙorafen a gaban kotun nasu kuma za su wallafa su ga al’umma.
Hakan na zuwa ne yayin da kwanaki 21 da aka ɗiba na bayar da damar ƙalubalantar sakamakon ya ƙare.
Jam’iyyu biyun dai na neman a sake nazari kan sakamakon zaɓen, wanda ya bai wa Adeleke na jam’iyyar Accord Party nasara.
