‘Ka kawo hujja ko ka janye kalamanka’, iyalan El-Rufa’i sun ba Ministan Tsaro kwana 7 kan zarginsa da hannu a rikicin kudancin Kaduna

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Malam Nasir Ahmad El-Rufai, ya bayar da wa’adin kwana bakwai ga Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa Gwabin (mai ritaya), da ya gabatar da wata hujja kan zarginsa ga tsohon gwamnan cewa ya shirya kashe-kashe a kudancin Kaduna ko kuma ya fito ya janye iƙirarin nasa.

Janar Musa dai ya zargi tsohon gwamnan ne na ɗaukar matakan da suka ƙarfafa rarrabuwar kai da taimaka wa matsalolin rashin tsaro a Jihar Kaduna a lokacin da yake gwamna daga shekarar 2015 zuwa 2023, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Ministan ya yi wannan iƙirari ne a wata hira da gidan talabijin na Channels a ranar 3 ga Satumba, 2026, inda ya bayyana halin da jihar ta tsinci kanta a ƙarƙashin gwamnatin El-Rufa’i a matsayin “iftila’i”.

Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Hon. Mohammed Bello El-Rufa’i – babban ɗan tsohon gwamnan a madadin iyalan El-Rufa’i, inda suka nemi Christopher Musa da ya fitar da wata hujja karɓaɓɓiya da za ta mara wa zargin nasa baya ko kuma ya fito fili ya janye tare da bayar da haƙuri ta inda ya furta kalaman.

Musa, a shirin Politics Today na Channels, ya ce mazauna kudancin Kaduna suna fushi da tsohon gwamnan kan kashe-kashen da aka samu a yankin yayin gwamnatinsa, yana mai bayyana hakan a matsayin iftila’i. “El-Rufa’i ya yi munanan abubuwa da dama a Kaduna. Ya raba jihar gida biyu. Ta haka, idan kai ɗan kudu ne, ba za ka je arewa ba ka yi rayuwa”, inji Janar Musa yayin hirar.

“Idan akwai abin da ya fi fushi. Ba za mu taɓa farin ciki da mutumin da ya kashe mana mutane ba da gangan,” inji shi a lokacin da aka tambaye shi ko har yanzu ‘yan kudancin Kaduna na fushi da El-Rufa’i. Haka kuma, ya zargi tsohon ministan Abujan da bayar da umarnin rushe gidajen mutanen da yake da wata rikici ta kai-da-kai da su.

Saidai, a sanarwar da gidan El-Rufa’in ya fitar, tsohon gwamnan ya musanta zarge-zargen nan da kuma neman a janye su.

Iyalan sun nuna damuwa kan tsokacin da ministan tsaron ya yi, inda suka bayyana zargin nasa a matsayin abin tayar da hankali kuma ta ce an yi shi ne ba tare da gabatar da hujja ba da za ta goyi bayan iƙirarin. Sun ce duk da cewa yana da ‘yancin bayyana ra’ayinsa, haka su ma suna da damar neman a ba su hujja kan zarge-zargen. Akan haka ne suka yi kira ga Janar Musa da ya janye kalaman nasa ta kafar da ya furta su kuma aka yaɗa wa duniya.

By Babaji

Leave a Reply