Abin da ya sa ba za a kama Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya ba – Jakadan MƊD

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya, Ambasada Jimoh Ibrahim, ya yi watsi da iƙirarin cewa akwai yiwuwar a kama Shugaba Bola Ahmed Tinubu ko kuma a sanya masa takunkumin zirga-zirga a Amurka yayin da ya halarci babban taron majalisar ɗinkin duniya.

Ibrahim ya ce, ofishin jakadancin Nijeriya ga MƊD bai samu wani saƙo daga gwamnatin Amurka ba da ke nuna cewa Tinubu ka iya fuskantar wani takunkumi a taron an UNGA, yana mai cewa shugaban Nijeriyar da iyalansa za su kasance cikin walwala a hedikwatar gunduma ta MƊD.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan bayani na zuwa ne yayin da aka sabunta iƙirari a kafafen sada zumunta cewa ta yiwu a kama Shugaba Tinubu ko a ɗauki matakin shari’a akansa muddin ya halarci taron UNGA karo na 81 a Birnin New York.

Jakadan, wanda kuma shi ne shugaban kwamitin kasafi da gudanarwa, ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi ta ofishin babban wakilin Nijeriya a Majalisar Ɗinkin Duniya a New York.

Ya kare matsayarsa ne da Sashe na 11 na kundin yarjejeniyar hedikwatar MƊD-Amurka ta 1947, wanda a cewarsa ta shar’anta wa hukumomin Tarayyar Amurka, jihohi da ƙananan hukumomi ƙaurace wa sanya takunkumi ga wakilin kowace ƙasa ta MƊD da iyalansa daga da kuma zuwa hedikwatar gunduma ta majalisar. Ya kuma ce, an faɗaɗa kariyar hatta akan jami’an MƊD, jami’an hukumomi na musamman da mutanen da aka gayyata zuwa hedikwatar bisa wani aiki na musamman.

A cewarsa, kafafen sada zumunta ba za su iya tabbatar da Tinubu ba a matsayin mai laifi ko su kama shi ko nawa ‘yan adawa suka bayar a matsayin lada, yana mai cewa babu wata iko da ta shar’anta kama shugaban a taron.

Haka kuma, jakadan ya buƙaci al’umma da su riƙa bambancewa tsakanin zarge-zargen aikata miyagun laifuka da yanke hukunci kai-tsaye kan samun mutum da laifi a dokance, yana mai ƙarawa da cewa halartar taron ka iya samun wakilcin shugaban ba tare da ya je da kansa ba.

Kazalika, ya yi kira ga ‘yan ƙasa da su cigaba bayar da kariya ga martabar Nijeriya a idon duniya tare da goyon bayan tsare-tsaren tattali da gwamnatin Tinubu ta samar domin ciyar da Nijeriya gaba.

By Babaji