Rundunar sojin Nijeriya ta sauya wa manyan kwamandoji wuraren aiki

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Rundunar Sojin Nijeriya ta sake yin wani gagarumin garambawul a shugabancinta, inda ta sauya wa wasu manyan kwamandojin soji wuraren aiki.

A wani ɓangare na sauye-sauyen, an tura Manjo Janar IA Ajose daga Hedikwatar Rundunar Soji domin jagorantar Rundunar Haɗin Gwiwa ta Arewa maso Gabas, Operation HADIN KAI, wadda ke yaƙi da Boko Haram da sauran ƙungiyoyin ta’addanci a yankin.

Ajose ya maye gurbin Manjo Janar AE Abubakar, wanda aka tura Cibiyar Tarihi da Makomar Rundunar Sojin Nijeriya, inda zai zama Shugaban Kwalejin Binciken Ayyukan Soji.

Rundunar ta ce sauye-sauyen, waɗanda Babban Hafsan Sojin Nijeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu, ya amince da su, na da nufin inganta ayyukan rundunar da kuma ƙarfafa shugabanci a muhimman wurare.

Daga cikin sauran sauye-sauyen akwai na Manjo Janar AM Umar, wanda aka naɗa Kwamandan Kwalejin Yaƙi ta Sojin Nijeriya, yayin da Manjo Janar UM Alkali ya koma Sashen Hulɗa tsakanin Sojoji da Fararen Hula.

Haka kuma, an naɗa Manjo Janar GS Muhammed a matsayin Darakta-Janar na ɓangaren Kuɗi na Rundunar Sojin Nijeriya, yayin da Manjo Janar JE Osifo ya zama Shugaban Hukumar Fansho ta Sojoji.

An kuma sauya wa wasu Birgediya Janar wuraren aiki, ciki har da Birgediya Janar MS Adamu, wanda zai jagoranci sabuwar Rundunar Birgediya ta 8, da Birgediya Janar MS Sule, wanda zai jagoranci Rundunar Birgediya ta 27 ta Task Force.

Rundunar ta buƙaci sabbin kwamandojin da su nuna ƙwarewa, shugabanci na gari da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.

Wannan sabon garambawul na zuwa ne ƙasa da shekara guda bayan da Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Laftanar Janar Waidi Shaibu a matsayin Babban Hafsan Sojin Nijeriya a watan Oktoban 2025.

Sauye-sauyen na zuwa ne a daidai lokacin da matsalolin tsaro ke ƙara ƙamari a wasu sassan ƙasar.

By ukarofi

Leave a Reply