Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi Allah-wadai da kisan gilla da aka yi wa shahararren mai tasiri a kafafen sada zumunta kuma mai sharhi kan harkokin siyasa, Ibrahim Khalil, wanda aka fi sani da Danshagamu.
Gwamnan ya umarci hukumomin tsaro da su gaggauta gano tare da kama wadanda ke da hannu a kisan, yana mai bayyana lamarin a matsayin abin firgitarwa da ba za a amince da shi ba.
News Point Nigeria ta ruwaito cewa Gwamna Yusuf ya kuma bukaci gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da gano dukkan wadanda ke da hannu a kisan tare da gurfanar da su a gaban shari’a.
Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, Darakta-Janar na Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Gidan Gwamnatin Kano, ya fitar ranar Laraba.
Gwamna Yusuf ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, abokansa da abokan hulɗarsa, yana addu’ar Allah Ya gafarta masa kura-kurensa, Ya kuma ba shi makwancinsa na Aljanna.
Ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su kwantar da hankalinsu tare da kauce wa ɗaukar doka a hannunsu, yana mai tabbatar musu da cewa gwamnati za ta ci gaba da aiki kafada da kafada da hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin jihar.
Haka kuma, Gwamna Yusuf ya umarci hukumomin tsaron da abin ya shafa, musamman rundunonin Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) da Rundunar ’Yan Sandan Nijeriya a Jihar Kano, da su ƙara kaimi wajen gano, kama da gurfanar da wadanda suka aikata kisan.
Ya jaddada cewa ba za a bari wani mutum ko wata ƙungiya ta ɗauki doka a hannunta ba.
