Majalisar Dokokin Ƙasa ta dakatar da hulɗa da Afrika ta Kudu kan hare-haren ƙyamar baƙi

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dokoki ta Ƙasa ta sanar da dakatar da kai ziyarar aiki zuwa ƙasar Afirka ta Kudu da shiga wasu harkoki da ƙasar ta shirya har sai illa ma sha Allahu, a wani yanayi na nuna damuwarta kan hare-haren ƙyamar baƙi da ‘yan ƙasar suke ƙaddamarwa akan ‘ya’yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashe da ke zama a can.

Hakan ya biyo bayan shawarwari tsakanin jagorancin majalisun dattawa da wakilai kan rahotannin da ke cewa ana kashe ‘yan Nijeriya, raunata su, ɗaiɗaita su da kuma tilasta musu barin harkokin kasuwanci da gidajensu da ma wasu kadarori sakamakon rikicin da ke cigaba da wakana.

A wata sanarwa da Akawon majalisar dokokin, Kamoru Ogunlana ya fitar, jagorancin ya ce ya damu da halin da kuma yadda Gwamnatin Tarayya da sauran masu ruwa da tsaki suka riƙa roƙon hukumomin Afirka ta Kudu kan su bai wa ‘yan Nijeriya da ‘yan wasu ƙasashe kariya da kuma gurfanar da waɗanda aka samu da hannu a laifin amma har yanzu ba a daina aikatawa ba.

Majalisar ta kuma bayyana yunƙurin gwamnatin tarayya kan al’amarin waɗanda daga ciki har da ƙoƙarin tallafa wa ‘yan Nijeriya da hakan ya shafa da samar da shirin dawo da su daga Afirka ta Kudu domin tseratar da rayuka da dukiyoyin al’umma.

A ƙarƙashin matsayar da majalisar ta cimma akwai dakatar da ziyarar aiki zuwa ƙasar kama daga kan kwamitoci, ‘ya’yan majalisa, jami’ai da kuma ma’aikata. Haka kuma, takunkumin ya haɗa da dakatar da taruka na ƙara wa juna sani, ganawa kan harkokin difulomasiyya da wasu hada-hada da ‘yan majalisar dokokin Afirka ta Kudu suka shirya ko jagoranta.

Wannan mataki na zuwa ne bayan watanni da aka sake sabunta kai hare-hare kan baƙi a Afirka ta Kudu duk da ɗaukar matakai da dama daga ɓangaren Nijeriya ciki har da kwaso ‘yan Nijeriya da dama daga ƙasar.

By Babaji

Leave a Reply