Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shahararren mawaƙin Nijeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Daɓido, ya bayyana cewa dangantakarsa da fitaccen attajirin nan Aliko Dangote ta samo asali ne tun lokacin ƙuruciyarsa, inda ya ce Dangote na da kusanci da iyalinsu tun kafin ya zama ɗaya daga cikin manyan ’yan kasuwa a Afirka.
Davido ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a Legas, yayin da yake magana kan dangantakarsa da Aliko Dangote. Ya ce Dangote ya daɗa yana hulɗa da mahaifinsa, ɗan kasuwa Adedeji Adeleke, kuma abotarsu ta yi shekaru masu yawa.
A cewar Davido, Dangote ya kasance kusa da iyalan Adeleke tun kafin ya yi fice a matsayin ɗaya daga cikin fitattun attajiran Afirka. Ya ce kusancinsa da iyalinsu ya kai har ga kasancewarsa cikin wasu muhimman abubuwan da suka shafi rayuwarsa tun daga haihuwa.
Davido ya ce, “Aliko Dangote ne ya kai mahaifiyata gida daga asibiti bayan ta haife ni.”
Wannan bayani ya nuna irin kusancin da ke tsakanin Dangote da iyalan Adeleke, wanda ya wuce alaƙar kasuwanci ko kuma ganawa a bainar jama’a kawai.
Mawaƙin ya ƙara da cewa abotar Dangote da mahaifinsa ta ci gaba da ƙarfafa tsawon shekaru, lamarin da ya sa shi ma ya saba da attajirin tun yana ƙarami.
Davido ya kuma bayyana cewa Aliko Dangote ya daɗe yana ba shi shawarwari kan yadda zai tafiyar da harkokin kuɗinsa.
A cewarsa, ɗaya daga cikin shawarwarin da ya fi yawan samu daga Dangote shi ne ya riƙa ajiye kuɗinsa tare da kula da yadda yake kashe su.
Ya ce, Dangote ya kasance yana maimaita wannan shawara gare shi tsawon shekaru, ba tare da la’akari da shekarunsa ko irin nasarar da ya samu ba.
“Duk lokacin da na gan shi, har yanzu yana ce min: ‘David, ka riƙa tara kuɗinka.’ Tun ina jariri yake gaya min haka,” inji Davido.
Mawaƙin ya ce wannan shawara ta ci gaba da kasancewa mai amfani a gare shi yayin da yake haɓaka sana’ar kiɗansa tare da faɗaɗa harkokin kasuwancinsa.
Davido ya samu maƙudan kuɗaɗe ta hanyar waƙoƙi, tallace-tallace, wasannin kiɗe-kiɗe da sauran harkokin kasuwanci, amma ya ce shawarar Dangote kan muhimmancin adana kuɗi da kula da su har yanzu tana da tasiri a rayuwarsa.
Baya ga dangantakarsa da Dangote, Davido ya kuma yi magana kan yadda yake kallon masu hannu da shuni da kuma yadda ake ganin rayuwar attajirai.
