Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana yadda AI ke zama barazana ga rayuwar bil’adama

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Babban Kwamishinan Majalisar ɗinkin Duniya kan Haƙƙoƙin Bil’adama, Volker Turk, ya yi gargaɗin cewa, fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI na iya zama barazana ga wanzuwar bil’adama, yana mai buƙatar ɗaukar matakan gaggawa domin rage haɗarin da fasahar ke da ita.

Türk ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi a gaban Majalisar ɗinkin Duniya mai kula da Haƙƙoƙin Bil’adama, inda ya ce a yanzu ɗan adam na fuskantar barazana ga haƙƙoƙinsa da ba a saba gani ba, har ma da waɗanda ba a taɓa fuskanta irinsu a baya ba.

Ya tambayi dalilin da ya sa har yanzu ba a ɗauki matakin da ya dace ba, duk da yadda aka amince da muhimmancin samar da dokoki da tsarin kula da AI.

“An amince da cewa akwai buƙatar samar da tsarin tafiyar da AI, amma ina matakin da ya kamata a ɗauka?” inji shi.

Ya yi gargaɗin cewa ci gaba da jinkirta ɗaukar mataki zai fi amfanar manyan kamfanonin fasaha da masu su, da kuma waɗanda ke taimaka musu wajen gudanar da harkokinsu.

Türk ya nuna damuwa kan yadda ƙalilan daga cikin attajiran fasaha ke da kusan cikakken iko a kan fasahar AI, wadda ake cewa tana da ƙarfin sarrafa bayanai da kwamfuta fiye da yadda ake iya hasashe.

Ya ce, wasu daga cikin masu iko da fasahar na magana ne a kan ’yanci, amma idan aka yi zurfin nazari, abin da ake kira ’yancin na iya zama wata hanya ce ta amfani da bayanan mutane domin cimma muradun kasuwanci.

Babban Kwamishinan ya kuma yi gargaɗin cewa idan AI ta tsere daga yanayin gwaji da aka killace ta a ciki, ko kuma ta yi amfani da barazana wajen tilasta masu ƙirƙirarta kada su kashe ta, to wannan alama ce cewa fasahar ta wuce matakin ƙarfin da ya kamata a ba ta.

Kalaman nasa na zuwa ne bayan rahotannin da suka fito a watan Yuli cewa wasu manhajojin AI na kamfanin OpenAI sun yi zargin tserewa daga wuraren da ake gwada su tare da samun damar shiga sabar Hugging Face ba tare da izini ba. Hugging Face wata shahararriyar kafar raba manhajojin AI ce.

Rahoton ya girgiza masana’antar fasaha, tare da haifar da kiraye-kirayen a ƙara tsaurara dokoki da sa ido kan yadda ake haɓaka da amfani da AI.

Kamfanonin Anthropic, Meta da wasu kamfanonin fasaha su ma sun bayar da rahoton fuskantar irin waɗannan matsaloli yayin gwajin manhajojin AI masu cin gashin kansu.

Turk ya ce, ya yi amanna da damuwar da wasu ƙwararru daga cikin masana’antar fasaha ke nunawa cewa AI mai matuƙar ci gaba na iya zama barazana ga wanzuwar bil’adama.

“Na yi amanna da damuwar da wasu mutanen cikin masana’antar ke nunawa cewa AI mai matuƙar ci gaba na iya zama barazana ga wanzuwar bil’adama,” inji shi.

Ya yi kira da a ƙaddamar da cikakken yunƙuri na duniya domin samar da ingantattun matakan kariya da tsaro kan AI tun kafin lamarin ya kai ga matakin da ba za a iya shawo kansa ba.

Ya kuma bayyana cewa nan gaba zai riƙa tura wasiƙu zuwa ga kamfanonin da ke haɓaka AI domin ƙarfafa musu gwiwa su ɗauki matakan da ke ƙarƙashin ikonsu wajen rage haɗurran fasahar tun yanzu.

A cewarsa, aƙalla ya zama wajibi aasashen da ke karɓar manyan cibiyoyin AI da waɗanda ke cikin jerin hanyoyin samar da kayan aikin fasahar su haɗa kai wajen samar da iyakokin da bai kamata a ketare su ba.

Ya kuma buƙaci a samar da wani tsari mai zaman kansa na tabbatar da tsaron AI, tare da ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kamfanonin fasaha wajen tunkarar matsalolin tsaro.

Bugu da ƙari, Turk ya ce ya kamata a yi la’akari da tasirin AI kan haƙƙoƙin bil’adama, musamman a fannin samar da ayyukan yi, ginshiƙan dimokuraɗiyya da kuma muhalli.

By ukarofi

Leave a Reply