Yanzu-yanzu: Tsohon shugaban PDP tsohon gwamnan Gongola, Bamanga Tukur ya rasu

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban jam’iyyar PDP na Ƙasa kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a Jamhuriya ta Uku, Bamanga Tukur ya rasu bayan shafe shekaru 90 a duniya.

Majiyoyin iyalansa ne suka tabbatar da rasuwarsa a ranar Asabar, duk cewa ba a bayar da cikakken bayanin kan al’amarin ba a nan take ga al’umma.

Marigayin, wanda aka haife shi a ranar 15 ga Satumban 1935, ɗan siyasa ne kuma jami’in gudanarwa wanda ya riƙe muƙamin gwamna a tsohuwar Jihar Gongola, wato wadda ta haɗa jihohin Adamawa da Taraba a yau, a lokacin Jamhuriyar Nijeriya ta Biyu.

Tukur ya fara hidimarsa ne a Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa (NPA), inda ya yi aiki a matsayin Janar Manaja daga alif 1975 zuwa 1982. Daga bisani ya koma harkar siyasa inda ya tsaya takara kuma ya lashe zaɓen gwamnan Gongola a 1983. Saidai wa’adinsa bai yi tsawo ba a muƙamin sakamakon an samu juyin mulki a shekarar a watan Disamba.

Bayan barin muƙamin, Bamanga Tukur ya faɗaɗa harkokinsa zuwa buɗe rukunin kamfanoni mai zaman kansa mai su a BHI Holdings, wanda aka fi sani da DADDO Group of Companies.

Ya koma aikin gwamnatin tarayya ne a tsakanin 1993 da 1995, a lokacin da ya riƙe muƙamin Ministan Masana’antu a ƙarƙashin gwamnatin soji ta Marigayi Janar Sani Abacha.

A shekarar 2012 ne aka naɗa marigayin a matsayin shugaban jam’iyyar PDP bayan samun goyon bayan Shugaba Goodluck Ebele Jonathan na wancan lokaci. Ya riƙe muƙamin har zuwa watan Junairun 2014 a lokacin da ya yi murabus bayan rikicin cikin gida ya dabaibaye jam’iyyar na tsawon lokaci.

Kazalika, Bamanga Tukur ya riƙe sarautar gargajiya ta Tafidan Adamawa. Bisa karrama hidimarsa ga ƙasa, Gwamnatin Tarayya ta ba shi kyautar ƙasa ta CON, wato Commander of the Order of the Niger. Haka kuma ya samu kyautar Commander of the Order of the Mono (COM) daga Jamhuriyar Togo. Ya rayu da matansa, ‘ya’ya da kuma jikoki.

By Babaji

Leave a Reply