Tsohon shugaban Saliyo ya koma gida bayan janye tuhumar cin amanar ƙasa

Spread the love

Tsohon shugaban ƙasar Saliyo, Ernest Bai Koroma, ya koma gida a ranar Lahadi bayan shafe sama da shekaru biyu yana zaune a Najeriya, sakamakon matakin da hukumomin ƙasarsa suka ɗauka na dakatar da shari’ar da ake yi masa kan zargin cin amanar ƙasa.

Koroma, wanda ya shugabanci Saliyo daga 2007 zuwa 2018, ya bar Najeriya zuwa Freetown bayan da aka kawo ƙarshen shari’ar da ta shafe tsawon lokaci tana rataye a kansa. Tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, wanda Koroma ya yi zaman gudun hijira a ƙasarsa, ne ya sanar da tafiyar tasa ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na ɗ.

Jonathan ya ce ya samu damar raka “abokinsa kuma ɗan’uwansa” Koroma domin fara tafiyar komawa Saliyo, yana mai bayyana farin cikinsa da ganin tsohon shugaban ya koma ƙasarsa cikin mutunci. Ya ce Najeriya ta kasance gida na biyu ga Koroma tsawon sama da shekaru biyu, sannan ya yaba da damar da aka samu na ba shi abota, goyon baya da kuma haɗin kai a lokacin da yake Najeriya.

Koroma ya bar Saliyo a watan Janairun 2024, bayan wata babbar kotu ta ba shi damar fita daga ƙasar domin neman magani, duk da cewa a lokacin yana fuskantar tuhumar cin amanar ƙasa. Daga baya ya zauna a Najeriya, inda aka karɓe shi tare da wasu jami’an gwamnatin ƙasar.

Tuhumar da ake yi wa tsohon shugaban ta samo asali ne daga zargin cewa yana da hannu a wani yunƙurin kifar da gwamnatin Shugaba Julius Maada Bio a watan Nuwamban 2023. A lokacin, wasu ‘yan bindiga sun kai hare-hare kan barikin sojoji da gidan yari, lamarin da ya ba da damar sakin kusan fursunoni 2,200, yayin da sama da mutane 20 suka rasa rayukansu.

Duk da cewa Koroma ya musanta hannu a yunƙurin juyin mulkin, yayin da lauyoyinsa suka yi watsi da tuhumar da ake masa, suna cewa an ƙirƙiro ta ne saboda dalilai na siyasa. Lamarin ya kuma faru ne a lokacin da ake ci gaba da takaddama kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasar na 2023, wanda ya ba Shugaba Bio damar samun wa’adi na biyu.

Sai dai a watan Yulin 2026, gwamnatin Saliyo ta sanar da dakatar da shari’ar da ake yi wa Koroma, matakin da ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan shari’o’in cin amanar ƙasa da suka jawo hankalin jama’a a ƙasar. Babban Lauyan Gwamnatin Saliyo, Alpha Sesay, ya bayyana cewa an cire batun daga jerin shari’o’in da kotu ke saurara, sannan aka kawo ƙarshen dukkan sharuddan belin da aka ɗora wa tsohon shugaban.

Gwamnatin ƙasar ba ta bayyana dalilin da ya sa ta janye shari’ar ba, amma matakin ya bude wa Koroma hanyar komawa Saliyo bayan sama da shekaru biyu da ya shafe a Najeriya. 

By ukarofi

Leave a Reply