Zuwa ga matasa: Kada mu bar siyasa ta raba mu, mu mayar da ita hanyar gina ƙasarmu

Spread the love

Ya ku matasan Nijeriya,

Assalamu alaikum wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Ina rubuta wannan wasiƙa ne a gare ku a daidai lokacin da siyasar Nijeriya ke sake ɗaukar wani sabon salo, yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. A hankali, gangamin siyasa na fara ƙamari, ’yan siyasa na fara neman goyon bayan jama’a, ƙungiyoyi na fara bayyana matsayinsu, yayin da kafafen sada zumunta ke ƙara zama filin muhawara da yaƙin neman zaɓe.

A irin wannan lokaci ne ya kamata mu, matasa, mu tsaya mu yi tunani sosai.

Domin gaskiyar magana ita ce: siyasa ba ta da matsala; abin da ke da matsala shi ne yadda ake yin siyasar.

Siyasa ita ce hanyar da ake bi wajen zaɓar waɗanda za su jagoranci al’umma, su tsara manufofin gwamnati, su raba albarkatun ƙasa, su samar da tsaro, ilimi, lafiya, aikin yi da sauran abubuwan da suka shafi rayuwar jama’a. Saboda haka, ba za mu iya cewa siyasa ba ruwanmu ba ce.

Siyasa ruwanmu ce. Mulki ya shafi rayuwarmu. Kuma makomar Nijeriya ta shafi kowane matashi.

Ya ku matasa, kada mu manta cewa mu ne mafi yawan waɗanda za su rayu da sakamakon shawarar da za a yanke a shekarar 2027. Zaɓin da za a yi yau zai iya shafar aikin da za mu samu gobe, irin ilimin da ’ya’yanmu za su samu, yanayin tsaron da za mu rayu a cikinsa, tattalin arzikin da za mu yi aiki a cikinsa da kuma irin Nijeriya da za mu bar wa waɗanda za su zo bayanmu.

Saboda haka, bai kamata mu shiga siyasa kamar masu kallon wasa ba. Ya kamata mu shiga cikinta kamar masu ruwa da tsaki.

Amma akwai wani babban abu da ya kamata mu fahimta: ba dole ba ne ka ƙi ɗan uwanka saboda kawai kuna goyon bayan ’yan siyasa daban.

Wannan shi ne babban kuskuren da matasa suke yawan yi.

A lokacin zaɓe, muna iya samun ra’ayoyi daban-daban. Wani yana goyon bayan jam’iyya A, wani yana goyon bayan jam’iyya B, wani kuma yana ganin wani ɗan takara ne ya fi dacewa. Wannan ba laifi ba ne. Dimokuraɗiyya tana buƙatar bambancin ra’ayi.

Abin da bai kamata ba shi ne mu mayar da bambancin ra’ayi zuwa ƙiyayya. Kada ka zagi wanda ba ya goyon bayan ɗan takaranka.

Kada ka ɗauki ɗan siyasar da kake goyon baya a matsayin wanda ba ya kuskure. Kada ka yarda wani ɗan siyasa ya gamsar da kai cewa duk wanda yake adawa da shi maƙiyinka ne. Kuma kada ka bari a yi amfani da kai wajen cutar da wani ɗan Nijeriya saboda bambancin ra’ayin siyasa.

Ya kamata mu koyi cewa ɗƙn siyasa abokin aiki ne na ɗan lokaci, amma ɗan uwa da ɗan ƙasa na dindindin ne.

Zaɓe zai wuce. Gangamin siyasa zai wuce. Taron jam’iyya zai wuce. Hotunan ’yan siyasa za su gushe daga kafafen sada zumunta. Amma mu zauna a wannan ƙasa tare. Za mu ci gaba da zama maawabta. Za mu ci gaba da zuwa kasuwa ɗaya, makaranta ɗaya, asibiti ɗaya da wuraren ibada.

Saboda haka, me zai sa mu bari siyasa ta lalata dangantakar da Allah ya gina tsakaninmu?

Ya ku matasa, lokaci ya yi da za mu daina kallon siyasa a matsayin hanyar samun kuɗin gaggawa kawai.

Eh, talauci yana da zafi. Rashin aikin yi yana da zafi. Matsin rayuwa yana da zafi. Amma bai kamata yunwa ta sa mu sayar da makomar kanmu ba.

Idan aka ba ka kuɗi domin ka halarci taron siyasa, ka karɓa idan doka da lamirinka sun yarda; amma kada ka sayar da ƙa’idarka da makomarka saboda kuɗin da zai ƙare cikin kwana ɗaya.

Idan aka ba ka abin hawa domin ka je taro, ka je idan kana so. Amma kada ka bari a mayar da kai kayan aikin tashin hankali.

Idan wani ɗan siyasa ya tallafa maka, ka gode masa. Amma ka tuna cewa goyon baya ba bauta ba ce. Kuma idan kana son wani ɗan takara, ka goyi bayansa da hujja, ba da zagi ba.

Ka bayyana abin da ya yi. Ka bayyana abin da ya kamata ya yi. Ka kwatanta manufofinsa da na sauran ’yan takara. Ka tambayi inda kuɗin aiwatar da manufofinsa zai fito. Ka tambayi yadda zai magance rashin tsaro. Ka tambayi yadda zai samar da aikin yi. Ka tambayi abin da zai yi game da ilimi, lafiya, noma, masana’antu da tattalin arziki. Ka tambayi yadda zai kare ’yancin ɗan ƙasa.

Wannan shi ne siyasar da Nijeriya take buƙata.

Ba siyasar “mu” da “su” ba. Ba siyasar addini da ƙabilanci ba. Ba siyasar zagi da cin mutunci ba. Ba siyasar yaɗa ƙarya ba.

Ya ku matasa, musamman waɗanda suke amfani da kafafen sada zumunta, ku tuna cewa kalmar da kuka rubuta cikin fushi na iya yaɗuwa cikin mintuna kaɗan ta haifar da abin da ba za ku iya gyarawa cikin shekaru ba.

Kada mu zama masu yaɗa labaran ƙarya. Kada mu yaɗa bidiyon da ba mu tabbatar da sahihancinsa ba. Kada mu yi amfani da hotunan da aka canja ko fasahar zamani ta AI wajen yaudarar jama’a. Kada mu yaɗa jita-jitar da za ta iya haddasa rikici tsakanin al’umma.

A wannan zamani, ilimin tantance sahihan bayanai ya zama wani ɓangare na kishin ƙasa.

Kafin ka danna “share”, ka tambayi kanka:

Shin gaskiya ne? Shin zai amfani al’umma? Shin zai iya jawo rikici? Shin zan iya kare abin da na rubuta idan aka tambaye ni? Idan amsar ta kasance a’a ce, kada ka yaɗa shi.

Haka kuma, ya kamata matasa su ƙara neman shiga cikin tsarin siyasa da kansu. Kada mu tsaya kawai wajen tallata ’yan siyasa a shafukan sada zumunta.

Mu shiga jam’iyyun siyasa. Mu shiga ƙungiyoyin farar hula. Mu shiga harkar wayar da kan masu zaɓe. Mu nemi muƙamai a cikin jam’iyyu. Mu tsaya takara idan mun cika sharuɗɗan doka. Mu shiga majalisun ƙananan hukumomi, jihohi da tarayya. Mu nemi wurin da za a ji muryarmu wajen tsara manufofin ƙasa.

Domin idan muka ƙi shiga inda ake yanke shawara, ba za mu yi mamakin yadda aka yanke shawara ba tare da mu ba.

Akwai bambanci tsakanin kasancewa mai goyon bayan ɗan siyasa da kasancewa ɗan siyasar da ke da manufa.

Na farko yana iya kare mutum komai ya yi. Na biyu yana kare ƙa’ida ko da wanda yake goyon baya ya yi kuskure.

Ya kamata mu zama na biyu.

Idan ɗan takaranka ya yi abin kirki, ka yaba masa. Idan ya yi kuskure, ka gyara shi. Idan ya kasa cika alƙawari, ka tambaye shi. Idan ya yi abin da ya dace da muradin jama’a, ka goyi bayansa.

Wannan ba cin amana ba ne. Wannan kishin ƙasa ne.

Ya ku matasa, kada ku bari wani ya gaya muku cewa ku matasa ne kawai da ya kamata a yi amfani da ku wajen ɗaukar tutoci, yin hayaniya ko kare ’yan siyasa a kafafen sada zumunta.

Ku ne makomar siyasar Nijeriya. Ku ne masu ilimi. Ku ne masu fasaha. Ku ne masu amfani da fasahar zamani. Ku ne ’yan kasuwa. Ku ne manoma. Ku ne ma’aikata. Ku ne malamai. Ku ne ’yan jarida. Ku ne masu shirya fina-finai. Ku ne masu tasiri a kafafen sada zumunta. Ku ne kuma waɗanda za su gaji wannan ƙasa.

Saboda haka, ku nemi matsayin da ya dace da ƙimar da kuke da ita.

Kada ku yarda a yi amfani da ku a matsayin kayan rikici. Kada ku ɗauki makami saboda siyasa. Kada ku kai wa wani hari saboda ya zaɓi ɗan takarar da ba ku so. Kada ku ƙona dukiyar jama’a. Kada ku lalata rayuwar wani saboda zaɓe. Kuma kada ku manta cewa babu wani ɗan siyasa da ya cancanci ku rasa rayuwarku saboda shi.

Idan wani ɗan siyasa ya rasa zaɓe, zai iya komawa gidansa ya ci gaba da rayuwa. Idan ya ci zaɓe, zai iya samu kariya da dama. Amma idan matashi ya rasa ransa saboda rikicin siyasa, babu wani zaɓe da zai dawo da shi.

Saboda haka, mu kiyaye rayukanmu. Mu kiyaye mutuncinmu. Mu kiyaye ƙasar nan.

A ƙarshe, ina kira gare ku da ku shiga zaɓen 2027 da cikakken tunani. Ku tantance ’yan takara bisa cancanta, halayya, tarihin ayyukansu da manufofinsu, ba wai saboda kyawun hotonsu a kafafen sada zumunta ko girman hayaniyar magoya bayansu ba.

Ku yi tambaya. Ku saurara. Ku bincika. Ku yi muhawara cikin mutunci. Ku zaɓa cikin ’yanci. Kuma ku girmama zaɓin wani.

Domin bayan an ƙidaya ƙuri’u, ba za mu ci gaba da zama APC, PDP, ADC, LP ko wata jam’iyya kawai ba.

Za mu sake zama ’yan Nijeriya. Kuma Nijeriya ta fi kowace jam’iyya girma. Ta fi kowane ɗan siyasa girma. Ta fi kowane zaɓe girma.

Ya ku matasa, 2027 ba wai kawai lokacin zaɓen shugabanni ba ne; lokaci ne na zaɓar irin makomar da muke son gadarawa kanmu da waɗanda za su zo bayanmu.

Mu shiga siyasa, amma kada siyasa ta shiga zuciyarmu har ta cire mana mutuncin ɗan Adam.

Allah Ya ba mu shugabanni nagari, Ya ba mu hikimar zaɓar waɗanda suka dace, Ya kare matasan Nijeriya daga fadawa tarkon tashin hankali, Ya kuma sa mu zama matasa masu amfani da ƙarfinsu wajen gina ƙasa, ba wajen rusa ta ba.

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD. 07066778190.

By ukarofi

Leave a Reply